8.2 Uku Saɓi
Wannan ma wasa ne dangin dara. Yawanci manya maza ke gudanar da shi. Amma akan samu lokutan da yara ke yi. Shi ma akan yi caca da ita, ta hanyar sanya kuɗi ko wani abin amfani ga wanda ya yi nasara.
7.2.1 Wuri da Lokacin Wasa
i. Akan gudanar da wannan wasa a filayen caca, da keɓaɓɓun wurare cikin kasuwanni. Yara sukan yi a gindin inuwoyin bishiyoyi a cikin unguwanni.
ii. Ana gudanar da wannan wasa da hantsi ko rana ko ma da yamma. Sai daiba a faye yin sa da dare ba.
7.2.2 Kayan Aiki
a. Ƙodagon goruba ko taura ko ƙwallon mangwaro ko duwatsu ko makamantansu.
8.2.3 Yadda Ake Wasa
Akan zana gidajen dara talatin da shida (36) ko a yi ‘yan gurabu yawan wannan adadi. Akan yi gidajen darar shida a tsaye, shida kuma a kwance, jere da juna reras. Daga nan kowa daga cikin ɓangarori biyu na masu wasa zai zaɓi nau’in ‘ya’yan da zai yi amfani da su (ko dai tsinke ko dutse ko ƙwallon mangwaro ko na taura ko ƙwadagon goruma da makamantansu). Kowane ɗan wasa zai ɗauki ‘ya’ya goma sha biyu (12).
Salon zubin uku saɓi ya bambanta da sauran wasannin dara. Domin shi bajewar ake yi ba kawai. A maimakon haka, masu wasa suna sanya ‘ya’ya ne ɗaya bayan ɗaya a gidajen da suke so. Yayin da mai tafiyar farko ya sanya ɗa a wani gida, sai kuma abokin tafiyarsa ya sanya ɗaya a wani gidan. A haka har sai ‘ya’yan kowanne sun samu shiga.
Wannan salon zubawa yana buƙatar iyawa da kuma nazari. Shi ya sa ma Bahaushe ke da Karin magana cewa: “Dara ruwa dara lissafi.” Wanda bai yi nazari ba, wato lissafi, yayin zubi, tuni za a ba shi ruwa. Mai wasan da ya sha ruwa a farko kuwa, zai yi wahala ya yi nasara. A garin neman toshe ruwa, mutum zai iya cin kan jaki idan bai lura ba. Wato ya jera uku yayin zubawa, wanda kuma ba a haka. Saboda haka, dole ya cire wanda ya san yana ƙarshe. Yawanci mai tafiyar fari zai yi ta ƙoƙarin saran baki ne. Abokin wasansa kuma zai yi ta ƙoƙarin toshe bakunan. Wannan ya yi daidai da Karin maganar Bahaushe da ke cewa: “Idan ba ka san dara ba toshe baki.”
Da zarar an gama jera ‘ya’ya, sai kuma a fara tafiya. Akan yi gaba ko baya ko kuma gefe da ɗa. Burin masu wasa shi ne su jera uku. Domin daga uku sun jeru, to an saɓa ke nan. Wanda ya saɓa kuwa zai ɗauke ɗan abokin wasansa ɗa a matsayin wanda ya cinye. Saboda haka, yayin da mai wasa ya jera ‘ya’ya biyu, sannan ya matso da na uku kusa yadda tafiyar gaba za ta saɓa, to ya sari baki ke nan. Abokin wasansa zai yi ƙoƙarin toshe wannan baki. Wanda ya saɓa zai duba idan abokin wasansa na da baki, zai lalata bakin ta hanyar ɗauke ɗaya daga cikin ‘ya’yan da ya sari baki da su. Idan kuma bakunan sun fi ɗaya, zai duba ya gaida na kwai wurin da zai iya buɗe randa. Zai yi hakan ne domin ya samu dammar sa ɓawa ko ta halin ƙaƙa bayan abokin karawarsa ya saɓa kuma ya ɗauka.
Yayin da ake wasa, kowane mai wasa zai yi fatan ya ta da danda. Danda dai salon jerin ‘ya’ya ne yadda duk tafiyar da mai wasa ya yi to saɓi ne. Wato yayin da ya saɓa da ɗa, ya sari baki ne a ɗaya ɓangaren.
Haka za a ci gaba da yi har sai an ƙarar da ‘ya’yan ɗaya daga cikin ‘yan wasan. Yayin da ‘ya’yan suka koma biyu kaɗai, mai wasa ya ci idan ya haɗa guda biyun wuri ɗaya. Idan kuwa ‘ya’yan mai wasa suka ƙare, ya rage saura ɗaya kaɗai, to duk tafiyar da ya yi zai ɗauki na abokin wasansa guda ɗaya. Amma wannan ya danganta da idan wasan ‘yar tafiya ɗaya ɗauka ce.
8.2.4 Tsokaci
Wannan wasa yana buƙatar zurfin tunani da nazari da nutsuwa. Saboda haka yana kaifafa basira tare da ƙara zurfin lissafi ga masu wasa. Sai dai akan yi amfani da wasan wurin yin caca.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.