Ticker

6/recent/ticker-posts

Efa-Efa

7.9 Efa-Efa 

Wannan wasa ne da yara maza da mata suka yi tarayya wurin yin sa. Yana da zubi da tsari irin na wasan Waran Warash. Bambancinsu kawai shi ne, a wasan Efa-Efa kowane yaro na ɗaukar lamba ne. Bayan an sanya yatsu ƙasa sai a ƙidaya. Idan yawan yatsun sun kasance daidai adadin lambar da yaro ko yarinya ya ɗauko ta ɗau, to ya fita ko ta fita. Misali biyar ko shida ko dai wata lamba.

A ƙasar Katsina ana irin wannan wasa. Sannan sun sanya wa sakamakon wannan wasa suna ‘motsawa.’

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

Post a Comment

0 Comments