Ticker

6/recent/ticker-posts

Dundunge

7.10 Dundunge

Wannan wasan yara maza da mata duka suna yin sa. Kimanin yara goma zuwa sama da haka ne suka fi gudanar da wannan wasa. Yana cikin jerin wasannin da ba sa tafiya da waƙa. Sannan yana buƙatar kayan aiki yayin gudanarwa.

7.10.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko a wani keɓaɓɓen fili da ba safai mutane ke zirga-zirga cikinsa ba.

ii. Akan yi wannan wasa da hantsi ko da yamma ko ma dadare, idan akwai farin wata.

7.10.2 KayanAiki

i. Ƙyalle ko tsumma (domin rufe idanun dundunge)

ii. Kara ko tsumagiya/bulaliya

7.10.3 Yadda Ake Wasa

Za a samu ɗan wasa guda ɗaya a rufe masa/mata idanu da ƙyalle ko tsumma ko dai wani abu mai kama da wannan. Sannan za a ba shi kara ko tsumagiya ya riƙe a hannu. Wato dai zai kasance tamkar makaho.

Ɗaya daga cikin masu wasa kuma zai riƙe wannan kara ko tsumagiya, tamkar ɗan jagora. Sunan wanda aka rufe wa ido dundunge. Mai masa jagora zai tambaye shi, yayin da shi kuma zai riƙa ba da amsa kamar haka:

Ɗan Jagora: Dundunge dundunge ka ci tuwo?

Dundunge: Eh.

 

Ɗan Jagora: Dundunge ka sha ruwa?

Dundunge: Eh.

 

Ɗan Jagora: Dundunge ka sha fura?

Dundunge: Eh.

 

Ɗan Jagora: Dundunge ina nawa?

Dundunge: Kare ya zubar!

 

Ɗan Jagora: To duk nan ‘ya’yana ne, kowa ka samu ka lafta, har da ni babbansu.

Da zarar an zo wannan gaɓa, kowa zai watse da gudu. Har shi ɗan jagoran ma zai kama gabansa. Daga nan dundunge kuwa zai riƙa bi yana laluɓawa da karansa. Duk wanda ya tarar, sai bugu. Su kuwa za su riƙa zagaya dundunge, wasu har zungurinsa za su riƙa yi suna faɗin:

Kowa ka samu ka lafta,

Kowa ka samu ka lafta!

Wani abin lura a nan shi ne, tambayoyin da ke sama an yi su ne a matsayin wasan maza, wato dundunge namiji ne. Idan kuwa a yara mata ne ke gudanar da wasan, to jinsin zai koma namata.

7.10.4 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce da suke bi domin motsa jikinsu. Yara da ma dundunge sukan sha gudu yayin gudanar da wasan.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

Post a Comment

0 Comments