Ticker

6/recent/ticker-posts

Dan Kurege

7.8 Ɗan Kurege

Yara maza da mata duk sukan gudanar da wasan ɗan kurege. Kimanin yara biyu zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa.

7.8.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko a cikin gida ko ƙofar gida, ko dai wani wuri da yara ke taruwa.

ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma. Wani lokaci akan yi shi da dare idan akwai wadataccen farin wata.

7.8.2 Kayan Aiki

i. Ƙasa

ii. Tsinke mai ɗan tsayi

7.8.3 Yadda Ake Wasa

Yara sukan tara ƙasa, sannan su tsikara tsinke tamkar dai yadda ake wasan na ɗiba. Sai kuma ɗaya daga cikin ‘yan wasa ya sanya hannunsa cikin wannan ƙasa. Hannun zai kasance ta baki-bakin ƙasar yadda bai kai ga wurin tsinken da aka tsikara a tsakiyar ƙasar ba. Ɗaya mai wasan kuma zai riƙa baje ƙasar kaɗan-kaɗan yana waƙa kamar haka:

Ɗan kurege mai tonon gyaɗata,

Ussha!

Ɗan kurege mai tonon gyaɗata,

Ussha!

Burin wannan mai baje ƙasa shi ne, a daidai lokacin da tsinken nan zai faɗi, to ya kama hannun da aka sanya a cikin ƙasar. Idan ya yi haka, to ya samu nasara ke nan. Idan kuwa tsinken ya faɗi, sai aka yi rashin sa’a wanda ya sanya hannunsa cikin ƙasar ya yi saurin zarewa yadda mai bajewa bai kama hannun ba, to bai ɓajewar ya faɗi. Yayin da kuma wanda ya sanya hannunsa cikin ƙasar ya zare hannun ba tare da tsinken ya faɗi ba, to nan ma ya faɗi.

7.8.4 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan yana buƙatar nutsuwa da taka-tsantsan yayin gudanar da shi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments