Ticker

6/recent/ticker-posts

Talili Tali Yambo

7.8 Talili Tali Yambo 

Wannan ma wasa ne da yara maza da mata suka yi tarayya wurin gudanar da shi. Yana ɗaya daga cikin rukunnen wasannin zaune da ke da waƙa. Kimanin yara huɗu zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa. Wani lokacin yawansu na iya kaiwa goma, ko ma sama da haka.

7.8.1 Wuri Da LokacinWasa

An fi gudanar da wannan wasa a dandali, da dare, musamman lokacin farin wata.

7.8.2 Yadda Ake Wasa

Yara na zama a tsarin da’ira. Amma sukan kasance kusa-kusa da juna. Sai kuma kowanne yaro ya ɗora ƙafarsa ta dama (idan wasan ‘yar dama ce) a cinyar wanda ke zaune gefe da shi. Idan kuwa wasan ‘yar hagun ce, to kowane yaro zai ɗora ƙafarsa ta hagu kan cinyar wanda ke zaune hagu da shi. Haka abin zai kasance wato an zagayo.

Da zaran an kamala ɗora ƙafa, za kuma a fara waƙa. Mutum ɗaya ko biyu ne za su riƙa ba da waƙa, saura kuwa na amsawa. Wanda ya fara ba da waƙar zai doki ƙafar da ke kan cinyarsa. Wanda aka doki ƙafar tasa shi ma zai doki ƙafar da ke kan cinyarsa. Haka abin zai yi ta tafiya. Wato dai kowa na dukan ƙafar da ke bisa cinyarsa, amma ɗaya bayan ɗaya. Sai dai dukan yakan kasance daidai gwargwado ne, ba mai zafi sosai ba. Amma duk da haka, yaran da ke da ƙarancin juriya har kuka sukan yi.

7.8.3 Waƙar Wasan Talili Tali Yambo

Bayarwa: Talili tali yambo,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Ɗan wasanmu na bara,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Bana ma ya dawo,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Yayinsa ake yi,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Kowa ya doki kansa,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Kowa ya doke ni sannu,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Ni ko na doke shi sosai,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Kowa ya ceci kansa,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Mu ga wanda bai iyawa,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Allah kashe makoɗa,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Gero ya samu kansa,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Allah kashe makoɗa,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Dawa ta samu kanta,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Allah kashe makoɗa,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Maiwa ta samu kanta,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Allah kashe makoɗa,

Amshi: Talili!

 

Bayarwa: Wake ya samu kansa,

Amshi: Talili!

Za a yi ta jero sunayen abinci da ake shukawa, har sai adadin waɗanda mai waƙar ya sani sun ƙare.

7.8.4 Tsokaci

Wannan wasa yana koya juriya ga yara. Wanda bai jure ba yayin wasan har kuka yakan/takan yi. Sannan wasan na ƙara wa yara sani game da nau’ukan abincin da Bahaushe ke shukawa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments