Ticker

6/recent/ticker-posts

Cankuloto-Kuloto

7.7 Cankuloto-Kuloto

Wannan wasa daidai yake da lakkuma-lakkuma lale ta fuskar zubi da tsari da kuma dokoki. Bambancinsu kawai shi ne waƙar da ake amfani da ita yayin taɓa guiwowin ‘yan wasa. Waƙar kuwa ita ce kamar haka:

Cankuloto-kuloto,

Cankulon balbalti,

Kai nabalbala kuka,

Mai jan kalangun ƙarfe,

Rina ta iya wayo,

Ta je tirken kwaɗi,

Ta ce wa Galadima,

Abin bana ya soma,

Igiyar ƙasa na ƙoto,

A rimin din-din,

Kwash!

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments