Ticker

6/recent/ticker-posts

Kasko-Kasko

7.6 Kasko-Kasko

Wannan wasa yana da zubi da tsari irin na wasan Lakkuma-lakkuma Lale.Abin da ya bambanta su kawai shi ne waƙar da ake gudanarwa a cikin wasannin. Waƙar wasan kasko-kasko ita ce kamar haka:

Kaso-kasko-kaso,

Kaskon yayadi,

Yayadi yadi ye,

‘Yarmalam ƙumbulashe,

Ƙumbulashe bakin manya,

Fara da ƙwaya,

Lailai da man guna,

Ata kwalaje bawan Ba’adare,

Tandu madara,

Tandun kalan-huɗe,

Ta bugalla alhim da bakwai,

Jaye guda!

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments