7.5 Lakkuma-Lakkuma Lale
Wannan wasa ne na yara maza da mata da ake gudanarwa a zaune. Yara biyu ma za su iya gudanar da wannan wasa. Sai dai yawan masu wasan na iya kasancewa biyar ko sama da haka.
7.5.1 Wuri Da Lokacin Wasa
Wannan wasa ne na dandali. Saboda haka, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin da akwai farin wata.
7.5.2 Yadda Ake Wasa
Yara sukan zauna su mimmiƙe ƙafafunsu. Daga nan ɗaya daga cikinsu zai fara waƙa tare da taɓa guiwowinsu ɗaya bayan ɗaya. Waƙar kuwa ita ce kamar haka:
Lakkuma-lakkuma yaki are,
Yaki are huwa dumbabe,
Dumbabe huwa Makka be,
Mukka be Madina be,
Asa ale aleti,
Ale tibil bileti,
Guju-guju babban zakara,
Na asshatunan danja,
Wush!
Duk guiwar ƙafar da wannan waƙa ta ƙare a kanta, to ƙafar ta fita. Saboda haka, mai ƙafar zai naɗe wannan ƙafa. Haka za a yi ta yi har sai kowa ya fita saura ƙafar mutum ɗaya. Daga nan za a ce ya zaɓa tsakanin sama ko ƙasa. Yayin da ya zaɓa sai a yi wannan waƙar tsakanin wurin da ya zaɓar (sama ko ƙasa) da kuma ƙafar da ba ta fita ba. Idan aka yi sa’a ƙafarsa ta fita, to ya dace. Idan kuwa ba ta fita ba (wato sama ta fita ko ƙasa) to ya faɗi ke nan. Don haka shi za a ci.
7.5.3 Sakamakon Wasa
Wadda ya faɗi a wannan wasa sakamakon da ke hawa kansa shi ne ci. Tun farkon wasa akan ƙiyasce ‘yar ci nawa ce. Wanda za a ci zai haɗa tafukan hannuwansa, wato bayan hannuwan na waje. Wanda zai ci kuma zai riƙa dukan bayan hannuwan da tafin hannunsa (har sai ya yi yawan dukan cin da aka ƙiyasce). Daga nan kuma wanda ake ci zai fara gociya. Wato zai yi ƙoƙari ɗauke hannunsa yayin da aka kawo duka. Idan ya ci sa’ ar gocewa dukan da aka kawo, to ya tsira. Idan kuwa bai goce ba, haka za a yi ta dukansa, har sai lokacin da ya goce. Mai ci kuma zai yi ta ƙoƙarin duka cikin gaggawa da yaudara yadda wanda ake ci ba zai iya gocewa dukan ba.
7.5.4 Tsokaci
Wannan wasa ne da ke buƙatar jarumta. Duk wanda ya faɗi zai fuskanci ci. Dole ne ya kasance mai juriya yayin da ake dukan hannuwansa don gudun dariya da zolayar abokan wasansa. Sannan wasan na koyar da ƙwarewa kamar yadda mai ci zai ta ƙoƙarin samun hannunuwan wanda yake duka a daidai. Wanda ake ci kuma zai yi ta ƙoƙarin gocewa.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.