Ticker

6/recent/ticker-posts

Caccayya

7.25 Caccayya

Wannan ma wasa ne da yara maza da mata duka na gudanarwa. Lokacin damana ake wannan wasa. Domin kuwa akan fara ne yayin da hadari ya taso aka fara kaɗa iska da ke nuna alamar za a yi ruwa. Ba shi da  takamaiman lokacin da aka keɓe domin gudanar da shi. Sannan ba a buƙatar wani kayan aiki yayin wannan wasa. Adadin masu yin sa kuwa, ya danganta da yawan yaran gida, ko yaran unguwa. Wani lokaci yaro ko yarinya guda ɗaya ma na wannan wasa.

7.25.1 Yadda Ake Wasa

Kamar yadda aka bayyana a baya, akan yi wannan wasa ne idan hadari ya taso. A wannan lokaci, yara sukan fito ƙofar gida, ko dandali. Za su fara waƙa da tsalle da tafi tare da buga ƙafafu a ƙasa. Wani lokaci za su ɗunguma cikin wannan yanayi su zaga kwararo-kwararo a cikin unguwa. Wasu daga ciki za su riƙa ba da waƙar, wasu kuwa na amsawa. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Allah Ya ba mu ruwa,

Amshi: Caccayya.

 

Bayarwa: Kogi ya jiƙe,

Amshi: Caccayya.

 

Bayarwa: Ni ma na jiƙe,

Amshi: Caccayya.

 

Bayarwa: Kowa ya jiƙe,

Amshi: Caccayya.

Bayarwa: Gona ta jiƙe,

Amshi: Caccayya.

 

Bayarwa: Allah ba mu ruwa,

Amshi: Caccayya.

7.25.2 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Da ma dai lokacin da hadari ya taso, sannan iska na kaɗawa, akan samu yanayi mai daɗi. Babba ma da zai samu sake, sai ya yi ta tsalle cikin wannan yanayi. Waƙar da yaran ke rerawa kuwa roƙon ruwa ce.

WASANNI A ƘASAR HAUSA 

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments