Ticker

6/recent/ticker-posts

‘Yar Canka

7.24 ‘Yar Canka 

Wannan ma na ɗaya daga cikin wasannin da yara maza da mata suka yi tarayya wurin gudanarwa. Ya kasance cikin rukunin wasannin zaune. Ba a ƙayyade wani lokaci ba na gudanar da wannan wasa. Akan yi si da hantsi ko da yamma ko da dare. Wasan ba ya tafiya da waƙa. Sannan akan gudanar da shi tsakanin mutane biyu ko sama da haka. Kayan aikin da ake amfani da shi kuwa yayin wannan wasa, dutse ne.

7.24.1 Yadda Ake Wasa

Masu wasa za su yi zane a ƙasa mai zagaye-zagaye, tamkar maganin sauro, ko a ce albasa. Wato dai wani zagaye cikin wani. Kowane mai wasa zai nemi tsakuwa ya ɗora kan layin farko da ke gabansa. Sannan zai nemi wata tsakuwar ya riƙe a hannu.

Mai wasa  na farko zai mayar da hannunsa baya. Sai ya sanya dutsen cikin ɗaya daga cikin hannayensa. Zai dunƙule hannuwan biyu sannan ya dawo da su gaba, ya miƙa wa abokin wasansa. Abokin wasan kuwa zai taɓa hannun da yake tunanin dutsen na ciki. Akan kira wannan nunawa da zai yi da suna canka.

Idan mai canka ya canka daidai, to ya ƙwace daga hannun mai yi. Saboda haka shi ne zai ɓoye dutse. Idan kuwa bai canka daidai ba, to wanda ya yi tafiya zai matsar da ‘yarsa zuwa kan layi na gaba, sannan ya sake ɓoyewa. Burin kowane mai wasa shi ne ‘yarsa ta isa tsakiya kafin aboki ko abokan wasansa.

7.24.2 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta wasa ƙwaƙwalwa gare su. Dole ne mai wasa ya yi tunani da nazari mai zurfi domin karantar zuciyar abokin wasansa. A haka ne zai iya hasashen hannun da ya sanya dutse. Akan karanci salon ɓoyo na mai wasa. Misali yakan canza hanu bayan tafiya ɗaya ko biyu, da dai sauransu.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments