Ticker

6/recent/ticker-posts

Allah Koro Ruwa

7.26 Allah Koro Ruwa

Wannan wasa yana da zubi da tsari irin na wasan Allah Ya Ba Mu Ruwa.Abin da ya bambanta su kawai shi ne bambancin da ke tsakanin waƙoƙin da ake rerawa cikin kowane wasa. A wasan Allah koro ruwa ana rera ƙaramar waƙa kamar haka:

Allah koro ruwa na koma rafi,

Ba na tsoron likita barai Ɗansanda.

Haka za a yi ta maimaita wannan waƙa.

7.26.1 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sannan yana ɗauke da addu’ar samun ruwan sama. Bayan haka kuma, akwai wani kurman baƙi da waƙar ta ƙunsa. Wannan kuwa shi ne faɗakarwa game da illoli da ke tattare da amfani da gurɓataccen rowan rafi. Ko dai ta hanyar ɗiba a sha, ko wanka ko wani abu makamancin haka. Shi ne yaran ke nuna cewa ba sa tsoron likita. Ke nan ba sa tsoron wata cuta da za ta kama su daga cikin ruwan. Bayan haka, ba sa tsoron Ɗansanda. Ke nan duk togaciyar da hukuma ke yi ba sa tsoronsa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments