Ticker

6/recent/ticker-posts

Dakin Tsuntsu

7.23 Ɗakin Tsuntsu 

Wannan wasa ne da yara maza da mata duka sukan gudanar da shi. Da wuya a furta adadin yaran da ke gudanar da wasan kai tsaye. Domin kuwa yaro ko yarinya guda ɗaya na iya yin wasan. Wani lokaci kuwa yaran sukan kai goma ko ma sama da haka. Wani lokaci yara sukan rera ƙaramar waƙa yayin wannan wasa. Iyaka kayan aiki da ake nema shi ne ƙasa mai damshi. Shi ya sa aka fi gudanar da wannan wasa lokacin damina, yayin da ƙasa ke da damshi. Sannan akan yi wannan wasa ne da hantsi ko da yamma. Yakan kasance kuma a cikin gida ko a ƙofar gida. Amma ba wasan dandali ba ne.

7.23.1 Yadda Ake Wasa

Kowanne daga cikin masu wasa zai kwarfaci ƙasa ya tara a gabansa. Daga nan zai ajiye ƙafarsa guda a ƙasa, ko dai ta dama ko ta hagu. Sai ya yi amfani da wani ɓangare na ƙasar da ya tara ya lulluɓe ƙafar. Zai sanya ƙasa mai yawa domin ta kasance mai kauri bisa ƙafar. Sannan zai daɓe ƙasar da hannunsa ko da bayan takalmi silifa saboda ya yi ƙarfi. Da zarar ya kammala, sai ya fara ƙoƙarin zare ƙafar a hankali. A wannan lokaci mai zarewa yakan yi waƙa kamar haka:

Ɗakin tsuntsu kar ka rushe,

In ka rushe ba na son ka.

 

Ɗakin tsuntsu kar ka rushe,

In ka rushe ka ci amana.

Burin yaro shi ne ya tsare ƙafarsa ba tare da ƙasar ta ruguje ba. Idan ya ci nasarar zare ƙafar daidai, gurbin da ya zare ƙafar zai samar da abin da ake kira ɗakin tsuntsu. Wannan shi ya kasance tamkar ɗakin kwana ga wasan yara.

Da zarar an kammala ɗaki, sai kuma a fara gina katangar gida. Ita ma dai akan yi amfani da ƙasa mai damshi ne a yi ta. Amma akan yi ɗan tattara ƙasa ne kawai a layi ba sai ta yi tudu sosai ba, a matsayin katanga.

Haka za a ci gaba da wasa. Wani lokaci akan yi ‘yartsana da ɓararren kara, a sanya cikin wannan ɗaki a matsayin masu gida. Yayin da aka gaji da wasa kuwa, za a baje waɗannan gidaje ne. Yawanci yara sukan ce:

“A ci moro, a ci moro.”

Sannan sai su baje ɗakunan da hannuwa ko ƙafafunsu.

7.23.2 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sannan wasan kwaikwayo ne yaran suke yi. Misali idan aka yi la’akari da kwaikwayon tsarin ginin gidajen Hausawa da suke yi. Kusan kowanne daga cikin masu wasa yana gina irin gidansu ne, ko wani gida da ya taɓa gani.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments