Ticker

6/recent/ticker-posts

‘Yar Sarki

7.19 ‘Yar Sarki

Wannan ma wasa ne da yara maza da mata suka yi tarayya wurin gudanarwa. Ana gudanar da shi ne a tsakanin yara uku. Wasan na da tsarin shugabanci da ya ƙunshi sarki da Ɗansanda da kuma ɓarawo. Wasa ne da ba ya tafiya da waƙa, sai dai ana buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi. Abin da ake amfani da shi wurin wannan wasa shi ne takalma.

7.19.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko a gidajen biki ko dai wani wuri da yara ke taruwa.

ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma ko da dare, yayin da akwai farinwata.

7.19.2 Yadda Ake Wasa

Kamar yadda aka bayyana a sama, yara uku ne suke gudanar da wannan wasa. Ɗaya daga cikinsu na kasancewa sarki, ɗaya kuwa Ɗansanda, sai na ukunsu ɓarawo. Ɓarawo zai riƙe takalma guda biyu sannan ya wurga su sama. Yayin da suka faɗo a buɗe duka gaba ɗaya, to ya ƙwace sarauta. Saboda haka zai zama sarki. Sarki kuma zai zama ɓarawo.

Idan kuma takalman suka kife gaba ɗaya, to ya  zama Ɗansanda. Ɗasanda kuwa zai zama ɓarawo. Idan kuwa aka yi rashin sa’a ɗaya daga cikin takalman ya kife, ɗaya kuwa ya ɓuɗe, to daidai yake da ya sake sata. Sannan yana nan a mazauninsa na ɓarawo. Saboda haka sarki zai umarci Ɗansanda ya masa hukunci. Kuma sarkin ne zai yanke irin hukuncin da za a masa.

7.19.3 Sakamakon Wasa

Duk ɓarawon da ya sake sata sarki zai yanke masa hukunci. Hukuncin kuwa shi ne duka da takalmi. Zai umarci Ɗansanda da ya masa duka iya wani adadi. Sannan dukan zai iya kasancewa mai zafi ko mai sanyi. Wannan ya danganta da ra’ayin sarki. Misali sarki zai iya cewa:

“Har yanzu dai ba ka bar sata ba ko?

Ɗansanda ba shi goma masu zafi da kuma biyar masu sanyi.”

A irin wannan yanayi, Ɗansanda zai masa duka goma masu zafi sannan ya masa biyar a hankali. Sannan ana dukan ne a bayan hannu. Ɓarawo zai miƙo bayan hannunsa. Ɗansanda kuwa zai yi amfani da takalmi wurin dukan.

7.19.4 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan yana ɗauke da wani saƙo na tari da muhimmanci da kuma Tasirin shugabanci. Baya ga haka kuma, wasan na faɗakarwa game da munin sata.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments