Ticker

6/recent/ticker-posts

Za Ni Za Ni Ye

7.18 Za  Ni  Za  Ni  Ye

Wannan ma wasa ne da yara maza da mata suka yi tarayya wurin aiwatar da shi. Yana da zubi da tsari irin na wasan Lakkuma-Lakkuma Lale. Abin da ya bambanta wasannin biyu kawai shi ne irin waƙar da ake yi a cikin kowanne. Waƙar wasan Za Ni Za Ni Ye ta kasance kamar haka:

Za ni za ni ye,

Za ni Kadisau,

Kadisan doki,

Dokin kara,

Kara na albasa,

Albashi kwaɗi,

Zuciyar damo,

Na faɗa kudu,

Na kuma na faɗa kudu,

Duk wanda waƙar ta faɗa kan ƙafarsa, to zai cire wannan ƙafa, tamkar dai a wasar Lakkuma-Lakkuma Lale.Sakamako da amfanin wannan wasa duk iri ɗaya ne da na Lakkuma-Lakkuma Lale

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

Post a Comment

0 Comments