Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwakwale

7.20 Ƙwaƙwale

Wannan ma wasa ne da yara maza da mata suka yi tarayya wurin gudanarwa. An fi gudanar da wasan lokacin damina. Wato yayin da ƙasa ke da damshi. Kimanin mutane biyar ne zuwa sama da haka suke gudanar da wannan wasa. Wani lokaci yawan na iya kasancewa ƙasa da haka. Amma idan haka ta faru, wasan ba ya daɗi.

7.20.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa cikin gida ko ƙofar gida ko wani wuri da ake samun taron yara.

ii. Ana wannan wasa ne da hantsi ko da yamma.

7.20.2 Kayan Aiki

i. Ƙwallon dabino

ii. Ƙwallon aduwa

iii. Ƙwallon taura

iv. Tsakuwa

v. Kuɗin ƙarfe (ƙwandala ko sile biyar ko kobo ko sisi da makamantansu)

7.20.3 Yadda Ake Wasa

Dukkanin yara, ban da guda ɗaya, za su toni rami amma ba mai zurfi sosai ba. Yaro guda da bai tona rami ba zai kasance riƙe da wasu daga cikin abubuwan da aka ambata a sama, daidai adadin ramukan da aka tona. Zai zo ya sanya abubuwan ɗaya bayan ɗaya a cikin waɗannan ramuka. Sannan ya mayar da ƙasa a rufe.

Sai kuma ya fara tambayar yaran ɗaya bayan ɗaya game da abin da ya rufe a ramin kowannensu. Bayan kowa ya faɗi abin da aka rufe a raminsa, sai kuma a ce a ƙwaƙwale. Don haka kowannensu zai tone raminsa, ya fiddo da abin da aka rufe ciki. Wanda ya faɗa daidai to ya ci nasara. Saboda haka, yana da maki guda. Haka za a ci gaba da wannan wasa ana ƙirga maki. Wanda ya fi kowa maki zai yi ta murna.

7.20.4 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da annashuwa da nishaɗi ga yara. Sannan yana koyar da nutsuwa da amfani da tunani domin gano ko tantance abubuwa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

Post a Comment

0 Comments