Ticker

6/recent/ticker-posts

Waran Warash

7.17 Waran Warash

Wannan wasa ne na yara maza da mata ke gudanarwa. Amma a wasu lokutan, akan samu mata ma suna yi. Yawan masu gudanar da shi na iya farawa daga biyu zuwa sama da haka, har zuwa biyar. Wasa ne da ba ya ɗauke da waƙa. Sannan ba a buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi.

7.17.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko a gida, musamman lokacin bukukuwa kamar bikin aure ko na haihuwa.

ii. Akan yi wannan wasa da hantsi ko da yamma ko kuma da dare.

7.17.2 Yadda Ake Wasa

Kowanne daga cikin masu wasa zai ɗauki suna; ko dai Jamilun ko Goron ko Goruba, ko Kash, ko Aminun. Daga nan za a fara wasa ta hanyar furta:

“Waran warash!”

Yayin da aka yi wannan furuci, kowa zai sanya yatsu a ƙasa, yawan adadin da ya ga dama. Ɗaya daga cikinsu zai ƙirga yatsun ɗaya ɓayan ɗaya ta hanyar ambaton:

Jamilun,

Goron,

Goruba,

Kash,

Aminun.

Zai riƙa taɓa yatsa a daidai lokacin da yake furta ɗaya daga cikin kalmomin. Haka zai bi kan yatsun masu wasa gaba ɗaya. Duk sunan da aka ambata a yatsar ƙarshe da masu wasa suka sanya, to wannan mai suna ya fita. Daga nan zai janye gefe ya zuba wa sauran masu wasa namujiya.

Yayin da wani ɗan wasa ya fita, waɗanda suka rage a ciki suna da damar canza suna domin ɗaukar sunan wanda ya fitan. Misali idan goruba ne ya fita, wani wanda ke da suna kash na iya cewa ya koma goruba ta hanyar furta:

“Na canza zuwa goruba.”

Haka za a ci gaba da fita ɗaya bayan ɗaya, har kowa ya fita a rage mutum ɗaya. Wannan da bai fita ba shi ne ya faɗi, saboda haka hukuncin nasa ya hau kansa. Wadda ya faɗi a wannan wasa sakamakon da ke hawa kansa shi ne ci. Tun farkon wasa akan ƙiyasce‘yar ci nawa ne. Wanda za a ci zai haɗa tafukan hannuwansa, wato bayan hannuwan na waje. Wanda zai ci kuma zai riƙa dukan bayan hannuwan da tafin hannunsa (har sai ya yi yawan dukan cin da aka ƙiyasce). Daga nan kuma wanda ake ci zai fara gociya. Wato zai yi ƙoƙarin ɗauke hannunsa yayin da aka kawo duka. Idan ya ci sa’angoce wa dukar da aka kawo, to ya tsira. Idan kuwa bai goce ba, haka za a yi ta dukansa, har sai lokacin da ya goce. Mai ci kuma zai yi ta ƙoƙarin duka cikin gaggawa da yaudara yadda wanda ake ci ba zai iya goce wa dukan ba.

7.17.3 Sakamakon Wasa

Sakamakon wanda ya faɗi wannan wasa shi ne ci, tamkar dai yadda aka yi bayani a sama.

7.17.4 Tsokaci

Wannan wasa yana buƙatar lissafi da zurfafa tunani. Domin kowane ɗan wasa zai riƙa karantar tunanin abokan wasansa. Zai yi tunanin yatsu nawa za su sanya, domin ya sanya daidai yadda shi ne zai fita. Sannan wasan yana koyar da juriya da zafin nama da kuma jarumta.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments