Ticker

6/recent/ticker-posts

Gidan Kurciya

7.16 Gidan Kurciya

Wannan wasa ne na tarayya tsakanin maza da mata. Wato maza da mata duk na gudanar da wannan wasa. Kimanin mutane ishirin zuwa sama ne suke gudanar da shi. Sai dai wasan ya fi daɗi idan aka samu yara da dama sun taru domin gudanar da shi. Akan rera waƙa cikin wannan wasa, amma ba a buƙatar wani kayan aiki yayin gudanar da shi.

7.16.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali da kuma makarantun boko.

ii. Akan gudanar da wannan wasa da dare da kuma rana, lokacin wasanni a makarantu.

7.16.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan yi da’ira, sannan su dafa kafaɗun juna. Wannan zai ba da damar a samu tazara a tsakankaninsu. Sunan waɗannan tazara gidan kurciya. Mai fara wasa zai/za ta riƙa shiga ta gidan kurciya ɗaya bayan ɗaya tare da yin waƙa, yayin da sauran masu wasa za su riƙa amsawa kamar haka:

Waƙa: Gidan kurciya,

Amshi: Shaya.

 

Waƙa: Wanda ya ɓata,

Amshi: Shaya.

 

Waƙa: Zai sha duka,

Amshi: Shaya.

 

Waƙa: Har da muntsini,

Amshi: Shaya.

Haka abin zai ci gaba, duk lokacin da mai wasa ya/ta tsallake gida ɗaya ba tare da ta/ya shiga ba, masu wasa za su ɗira masa dundu. Haka mai wasa zai/za ta ci gaba har sai ta/ya gama yin sa/ta. Daga nan kuma sai mai yi nagaba ya/ta karɓa.

7.16.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki tare da samar da nishaɗi ga yara. Sannan yana koyar da nitsuwa da kuma bin ƙa’ida.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments