Ticker

6/recent/ticker-posts

Sai Ka Yi Rawa A Nan

7.11 Sai  Ka Yi Rawa A Nan

Wannan ma wasa ne da yara maza da mata suka yi tarayya tsakanin yara maza da mata wurin gudanar da shi. Kimanin yara huɗu ne zuwa sama suke gudanar da wannan wasa. Yana tafiya da waƙa, sannan ana buƙatar kayan aiki kafin gudanar da shi. An fi gudanar da wannan wasa lokacin da dare kamar sauran tashen ƙasar Hausa.

7.11.1 Kayan Aiki

i. Kayan maza da suka haɗa da babbar riga da hula da makamantansu

ii. Auduga (a matsayin gemu)

iii. Wani abu mai danƙo da za a iya laƙa auduga da shi

iv. Sanda

7.11.2 Yadda Ake Wasa

Yara (ko da maza ne ko mata) sukan samu ɗaya daga cikinsu ya zama Alhaji. Zai/za ta yi shigar namiji tsoho. Wato zai sanya babbar riga da hula da rawani. Sannan za a masa gemun auduga. Daga nan Alhaji zai riƙe sanda ya riƙa dogarawa.

Yayin da aka je wurin da za a gabatar da tashe, Alhaji zai fara rawa tare da dogara sandarsa da kuma ɗan sunkuyo, tamkar dai tsoho ne na gaske. Sauran yara kuwa za su fara waƙa, Alhaji yana amsawa. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Alhaji,

Alhaji: Eye.

Bayarwa: Sai ka yi rawa a nan,

Alhaji: A gaban‘ya’yana?

 

Bayarwa: Alhaji,

Alhaji: Eye.

 

Bayarwa: Sai ka yi rawa a nan,

Alhaji: A gaban matana?

 

Bayarwa: Alhaji,

Alhaji: Eye.

 

Bayarwa: Sai ka yi rawa a nan,

Alhaji: A gaban jikoki?

 

Bayarwa: Alhaji,

Alhaji: Eye.

 

Bayarwa: Zan ba ka Talatuwa,

Alhaji: Talatuwar ta yarda?

 

Bayarwa: Alhaji,

Alhaji: Eye.

 

Bayarwa: Zan ba ka buhun gyaɗa,

Alhaji: Amaro zan soya.

 

Bayarwa: Alhaji,

Alhaji: Eye.

 

Bayarwa: Zan ba ka dubu biyar,

Alhaji: Kanti zan buɗe.

 

Bayarwa: Alhaji,

Alhaji: Eye.

7.11.3 Tsokaci

Wannan wasa angina shi ne bisa raha da nishaɗi. Sannan yana nuna cewa, bai kamata babba ya aikata wani abu ko ya faɗi wata magana marar kyau a gaban yara ba. Domin kuwa yayin da manya ke magana, yara sun kasa kunne suna saurare. Duk abin da manyan kuwa suka yi, shi yara ke kwaikwaya.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments