Ticker

6/recent/ticker-posts

Tserel

7.12 Tserel 

Wannan ma wasa ne wanda yara maza da mata duka suna yi. Akan iya yin tseren tsakanin kimanin yara biyu kacal. Sai dai idan aka samu taron yara, abin ya fi armashi. Wasan ba ya tafiya da waƙa, duk da ma wani lokaci yara na yin kirari da zuga ga masu tserel saboda su dage kada a bar su a baya.

7.12.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali da kuma makarantun boko.

ii. Akan gudanar da wasan  da hantsi ko da yamma ko da dare.

7.12.2 Yadda Ake Wasa

Masu tserel za su jeru a layi ɗaya. Sannan za su duƙa su kafa guiwowin ƙafafunsu ɗaɗɗaya a ƙasa, su kuma dafa ƙasa. Daga nan za a ƙirga daga ɗaya zuwa uku. Da zarar an kammala wannan ƙirge yara za su ruga a nakare zuwa wurin taɓawa. Da zarar mutum ya taɓa zai yi ƙoƙarin dawowa da gudu idan tserel ɗin ‘yar zuwa da dawowa ce. Wanda ya riga dawowa duk shi ne na ɗaya. Idan kuma ‘yar zuwa ce kawai, wanda ya riga taɓawa shi ne na ɗaya.

7.12.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. A makarantun boko ma akan haɗa wasanni da kuma gasanni da suka shafi tserel.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments