‘Yartsana

    7.1 ‘Yartsana 

    Wannan wasa ne da yara maza da mata suka yi tarayya wurin gudanar da shi. Wasa ne na yara ƙanana, wato masu shekarun da ba su wuce shida ba. Wannan na iya zama dalilin da ya sa yara maza da mata duka ke gudanar da wannan wasa, sannan tare a lokaci da dama. Wasan nasu tare (maza da mata) na kasancewa sakamakon shekarunsu bai kai lokacin da bambancin jinsi ke tasiri a kansu sosai ba.

    7.1.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Wannan wasa ba na dandali ba ne. Akan gudanar da shi ne cikin gida, ko zauren ƙofar gida. Idan cikin gida ne akan samu wuri mai inuwa, kamar ƙarƙashin bishiya ko wani wuri makamancin wannan.

    ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma.

    7.1.2 Kayan Aiki

    i. ‘Yardadar kara ko tsolon rake ko taɓo ko makamancin wannan

    ii. Ƙyallaye ko tsommokara ƙanana

    iii. Marafen kwalabe da na goruna (a matsayin kayan jere da kwanuka)

    iv. Kwalin sukari ko na jingam ko makamancin haka (a matsayin akwati ko gado)

    v. Ganyen tafasa ko dai ganyen wata itaciya

    vi. Ruwa

    vii. Tukunyar laka

    viii. Tsinkaye

    7.1.3 Yadda Ake Wasa

    Wannan yana ɗaya daga cikin wasannin yara da ke ɗaukar tsawon lokaci ba tare da an kai ƙarshensa ba. Wasu lokuta har akan yi kwana da kwanaki ba tare da an kammala shi ba. Masu wasa sukan samo ‘yar dadar kara ko wani abu makamancin haka. Za a yi wa wannan ‘yar dada kwalliya da ƙyallaye tamkar dai wata budurwar gaske. Daga nan kuma za a nemi wata ‘yar dadan a yi mata shigar maza a matsayin saurayin da zai auri waccar budurwa da aka yi wa kwalliyar mata. Amma wani lokaci akan sanya yaro ɗaya daga cikin ‘yan wasan ne ya kasance mijin Yartsanar.

    Wasan Yartsana ya bambanta daga wuri zuwa wuri. Sannan ya danganci yaran da suke gudanar da wasan. Wani lokaci yara sukan kwaikwayi dukkanin al’adun aure kamar dai yadda suke gani a wurin manya. Wannan ya haɗa da zuwa hira/zance, da sauran al’adun neman aure da kuma na ɗaurin aure da tarewar amarya. Wani lokaci kuma yara sukan nuna gidan auren ne kawai. Wato ɗakin amarya da kuma mijinta, da sauran kayan taskar gida da wurin dafa abinci da makamantansu.

    A gidan amaryar kuwa (wato Yartsana), za a ci gaba da nuna yadda tsarin zamantakewa take tsakanin miji da mata. Masu wasa za su shirya ɗaki tsaf, har da jere da shimfiɗar gado da kuma kujeru. Sannan akan samar da wurin dafa abinci. Akan samu duwatsu uku a haɗa murhu. Sannan a ɗora tukunyar laka tawasa ko wani gwangwani a matsayin tukunya. Za kuma a sanya tsinkaye a matsayin itatuwan dafa abinci. Yawanci abincin na kasancewa naƙasa (tuwo). Miya kuwa akan sami ganyen tafasa ko wata itaciya a yayyanka domin haɗa ta.

    A lokuta da dama akan sami ɗaya daga cikin masu wasa ya/ta riƙa muryar amarya, ɗaya kuma na muryar ango. Misali, lokacin da duk aka gama abinci aka zuba a kwanuka, mai muryar amarya zai/za ta miƙo wurin da za a aje wa mijin sannan ta furta magana misali:

    “To mai gida ga abinci.”

    Mai yin muryar mai gidan kuma zai/ za ta ci gaba da amsa mata. Haka dai wannan wasa yake kasancewa. Wato yana ci gaba da bin rayuwar ma’aurata daki-daki. Wani lokaci har a kai ga gacin amarya ta haihu, don haka za a shirya bukin suna.

    7.1.4 Wasu Al’adu Da Ɗabi’u Da Ake Nunawa A Wasan ‘Yartsana

    i. Al’adun neman aure da suka shafi nema da bayarwa da ɗaurin aure da kai amarya

    ii. Kwalliyar amarya da ango

    iii. Tsarin gidan amarya

    iv. Nauyin da ke kan maigida da suka haɗa da nemo abinci da magani da makamantansu

    v. Nauyin da ke kan matar gida da suka haɗa da dafa abinci da share gida da makamantansu

    vi. Zamantakewar gidan aure

    7.1.5 Tsokaci

    Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Ya kasance tamkar hoto ko madubi na hango tsarin aure da zamantakewar auren Hausawa.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.