Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Diba

7.2 Na Ɗiba

Wannan wasa ne da yara maza da mata suka yi tarayya a gudanar da shi. Kimanin mutane biyu zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa.

7.2.1 Wuri Da LokacinWasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko a cikin gida ko ƙofar gida, ko dai wani wuri da yara ke taruwa.

ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma. Wani lokaci akan yi shi da dare idan akwai wadataccen farin wata.

7.2.2 Kayan Aiki

i. Ƙasa

ii. Tsinke mai ɗan tsayi

7.2.3 Yadda Ake Wasa

Akan tara ƙasa daidai gwargwado, sai kuma a tsikara tsinke a tsakiyar ƙasar. Tsinken zai kasance mai tsawo yadda zai ratsa ƙasar ya iso har ƙasa. Daga nan yara za su fara ɗiban ƙasar ɗaya bayan ɗaya. Duk wanda lokacin ɗibansa ya zo, zai riƙa ɗiba tare da waƙa kamar haka:

Na ɗiba,

Na kuma na ɗiba,

Na sake na ɗiba,

Ga ladana.

Wannan na nuna cewa, mai ɗiban ƙasar zai ɗiba ne sau huɗu. Haka za su ci gaba da ɗiba ɗaya bayan ɗaya, kowa yana tara ƙasar da ya ɗiba a gabansa. Za su riƙa yi suna matuƙar taka tsantsan da tsinken da aka tsikara a tsakiya domin kada ya faɗi. Za ta kai lokacin da zai zama ‘yar ƙanƙanuwar ƙasa ce take riƙe da tsinken. A wannan lokaci, yara za su riƙa ɗibar ƙasar a hankali, sannan kaɗan-kaɗan. Duk wanda wannan tsinke ya faɗi a lokacin ɗibansa, to ya faɗi. Sannan shi za a daka.

7.2.4 Sakamakon Wasa

Sakamakon wanda ya faɗi a wannan wasa shi ne dala. Za a tara ƙasa, sannan wanda za a daka ya ɗora tafin hannunsa a kai. Masu daka kuwa za su riƙa dunƙule hannusu na dukan kan bayan hannun nasa. Wannan ya danganta da yawan dakan da suka ƙayyade za su yi.

7.2.5 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan yana buƙatar nitsuwa da taka tsantsan yayin gudanar da shi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments