Ticker

6/recent/ticker-posts

Ga Mairama Ga Dauda

6.93 Ga Mairama Ga Dauda

Wannan ma wasan tashe ne na yara mata. Yana ɗaya daga cikin wasannin da ke buƙatar kayan aiki. Da yake wasan tashe ne, an fi gudanar da shi da dare, bayan an sha ruwa, wato cikin watan azumi. Kimanin yara takwas zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa.

6.93.1 Kayan Aiki

i. Tabarma

ii. Kayan sawa namaza da namata (shigar amarya da ango)

iii. Kwanukan abinci

6.93.2 Yadda Ake Wasa

Akan samu yara guda biyu. Ɗaya ta yi shigar amarya, ɗaya kuma ta yi shigar ango. Amaryar akan kira ta da Mairama, angon kuwa Daudu. Yayin da aka shiga gida domin tashe, akan shimfiɗa tabarma sannan a jera kwanukan abinci, tamkar dai akwai abincin gaske a ciki. Sai kuma Mairama da Daudu su zauna bisa wannan tabarma.

Sauran yara za su riƙa waƙa tare da tafi. Zabiya za ta fara ba da waƙa yayin da saura za su riƙa amsawa. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Ga Mairama ga Daudu,

Amshi: Ga Mairama.

 

Bayarwa: Ga Mairamarmu sharifiya,

Amshi: Ga Daudu.

 

Bayarwa: Ga Daudunmu sharifi,

Amshi: Ga Mairama.

 

Bayarwa: Don Allah ba shi ruwa ya sha,

Amshi: Ga Daudu.

 

Bayarwa: Don Allah ba shi fura ya sha,

Amshi: Ga Maryama.

 

Bayarwa: Don Allah ba shi kunu ya sha,

Amshi: Ga Daudu.

 

Bayarwa: Sai in taka rawa in rausaya,

Amshi: Ga Maryama.

Haka za su yi ta yi har sai lokacin da aka sallame su.

6.93.3 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi musamman ga masu kallonsa. Yana nuni ga rayuwar aure tsakanin mata da miji. Wannan ya haɗa da yadda mace ya dace ta riƙa kyautata wa miji.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments