Ticker

6/recent/ticker-posts

Tama Yaki Tama

6.94 Tama Yaki Tama

Wannan wasan mata ne da ke tafiya da waƙa. Kasancewarsa wasan gaɗa na dandali, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata. Ba ya buƙatar kayan aiki yayin gudanarwa. Adadin yaran da ke gundanar da shi na iya kaiwa goma ko ma sama da haka.

6.94.1 Yadda Ake Wasa

Yara sukan yi layi ne, saɓanin mafi yawan wasannin gaɗa inda suke tsayuwa a tsarin da’ira. Daga nan za su fara yin waƙa tare da tafi. Yayin da suke waƙar, za su ɗan riƙa motsa ƙafafu zuwa gefe da gefe ko kuma gaba da baya.

Tsarin ba da waƙar kuwa shi ne, ta farko bisa layi za ta zo ta rera ɗiya ɗaya, saura kuma su yi mata amshi. Daga nan za ta koma cikin layi. Wadda ke tsaye gefenta kuma za ta fito ita ma ta yi haka nan. Haka za a yi ta yi har a je ƙarshen layin, sai kuma a sake dawowa daga fari. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Tama yaki tama,

Amshi: Galadima.

 

Bayarwa: Wasa ba faɗa ba,

Amshi: Arerere.

 

Bayarwa: Filin gorin miji ne,

Amshi: Galadima.

 

Bayarwa: Ke naki me yake yi?

Amshi: Arerere.

Bayarwa: Ni nawa ɗan majemi,

Amshi: Arerere.

Bayarwa: Ya jeme ki,

Amshi: Galadima.

Bayarwa: Ku ci jima ku kwana jima,

Amshi: Arerere.

 

Bayarwa: Ni nawa ɗan masaƙi,

Amshi: Galadima.

Bayarwa: Ya saƙe ki,

Amshi: Arerere.

Bayarwa: Ku ci saƙa ku kwana saƙa,

Amshi: Galadima.

 

Bayarwa: Ni nawa ɗan manomi,

Amshi: Arerere.

Bayarwa: Ya nome ki,

Amshi: Galadima.

Bayarwa: Ku ci gero ku ci dawa,

Amshi: Arerere.

 

Bayarwa: Ni nawa ɗan maharbi,

Amshi: Galadima.

Bayarwa: Ya harbe ki,

Amshi: Arerere.

Bayarwa: Ku ci harbi ku kwana harbi,

Amshi: Galadima.

 

Bayarwa: Ni nawa ɗan maɗinki,

Amshi: Arerere.

Bayarwa: Ya ɗinke ki,

Amshi: Galadima.

Bayarwa: Ku ci ɗinki ku kwana ɗinki,

Amshi: Arerere.

 

Bayarwa: Ni nawa ɗan mahauta,

Amshi: Galadima.

Bayarwa: Ya yanke ki,

Amshi: Arerere.

Bayarwa: Ku ci nama ku kwana suya,

Amshi: Galadima.

 

Bayarwa: Ni nawa ɗan maƙeri,

Amshi: Arerere.

Bayarwa: Ya ƙera ki,

Amshi: Galadima.

Bayarwa: Ku ci ƙira ku kwana ƙira,

Amshi: Arerere. 

6.94.2 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga masu gudanarwa. Waƙar wasan kundi ce da ke kundace sana’o’in gargajiya na Hausawa. Yara na nuna muhimmancin sana’a ga ɗa namiji. Wanda har ta kasance abin taƙama ne a ce mijinsu na da sana’a.

WASANNI A ƘASAR HAUSA 

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments