Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsakiyata Ta Tsinke

6.92 Tsakiyata Ta Tsinke 

Wannan ma wasan gaɗa ne na dandali. Kimanin yara mata goma zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Kasancewar wannan wasa na dandali, an fi gudanar da shi da dare, lokacin farin wata. Ba a buƙatar kayan aiki domin gudanar da shi. Sannan yana tafiya da waƙa.

6.92.1 Yadda Ake Wasa

Yara sukan yi da’ira, sannan su kakkama hannuwan juna. Sai kuma su tsuguna gaba ɗayansu. Sannan za su fara waƙa kamar haka:

Tsakiyata ta tsinke,

A ɗakin masoyina,

In sunkuya in ɗauka,

Abin ma da kunya,

Ba da kunya ba,

Ala tsine ‘yar kunama,

A cikin duhun ciyawa.

Da zarar sun zo wannan gaɓa kowacce za ta tashi. Za su riƙa tsalle tare da zagayawa ba tare da sun sake hannuwan juna ba. Wannan zai sa su riƙa fincikar juna. Za su riƙa waƙa kamar haka:

A shinkafa ta cin-cin,

A shinkafa ta shari gyaɗa.

Wanda ya faɗi mijin kuliya,

Wanda ya faɗi mijin kuliya.

Da zarar ɗaya daga ciki ta faɗi, to za a rufe ta da tsokala.

6.92.2 Sakamakon Wasa

Sakamakon wannan wasa shi ne tsokala. Duk wadda ta faɗi yayin wannan wasa za a rufe ta da tsokala. Za a riƙa mata waƙa kamar haka:

Mijin kuliya,

Mijin kuliya. 

6.92.3 Tsokaci

Wannan wasa ne da ke samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su. Waƙar da ke ciki kuwa tana nuni ga al’adar Bahaushe ta kunya.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments