Ticker

6/recent/ticker-posts

Fadi Mana

6.91 Faɗi Mana 

Wannan ma wasan yara mata ne da ke da zubi da tsari irin na wasan kwalba-kwalba dire. Abin da ya bambanta su kawai shi ne irin waƙar da ake rerawa cikin kowanne. Ga yadda waƙar wasan faɗi mana  take:

Mai Direwa: In faɗiye-faɗiye,

Ba su Cilli: Faɗi mana.

 

Mai Direwa: In faɗi mai so na?

Ba su Cilli: Faɗi mana.

 

Mai Direwa: Ku kuka sa ni,

Ba su Cilli: Faɗi mana.

 

Mai Direwa: To kar ku ga laifina,

Ba su Cilli: Faɗi mana.

 

Mai Direwa: To kada ku ga haukata,

Ba su Cilli: Faɗi mana.

 

Mai Direwa: Babu munafunci,

Ba su Cilli: Faɗi mana.

 

Mai Direwa: Babu ɓoye-ɓoye,

Ba su Cilli: Faɗi mana.

 

Mai Direwa: Kabiru yana so na.

Ba su Cilli: Faɗi mana. 

6.91.1 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su. Bayan haka, wasan na ba su dama su bayyana sunayen masoyansu. Wannan saƙo ne zuwa ga iyaye da masu da ma duk wani da zai saurari waƙar wasan, da kuma ƙawayen mai wannan waƙa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments