Ticker

6/recent/ticker-posts

Kifi-Kifi

6.90 Kifi-Kifi 

Wannan ma wasan dandali ne na yara mata. Kimanin yara goma zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Wasan yana da sigar kwalba-kwalba dire ta fuskar cilli da direwa. Amma sun bambanta ta ɓangarori da dama. Kasancewar wasan  na dandali, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata. Ba a buƙatar wani kayan aiki yayin gudanar da shi. Sannan yana tafiya da waƙa.

6.90.1 Yadda Ake Wasa

Yara za su rabu kashi biyu. Za su kasance suna fuskantar juna. Amma za su bar tazara mai ɗan faɗi a tsakaninsu. Daga nan yara biyu za su fito tsakiya, waɗanda kuma su ne masu direwa. Daga nan za a fara waƙa tare da tafi. Waɗannan yara biyu na tsakiyar fili za su riƙa faɗawa hannun waɗanda ke tsattsaye. Ɗaya za ta faɗa wa ɓangare ɗaya, ɗayar kuma za ta faɗa ɗaya ɓangaren. Waɗanda ke tsayen kuwa za su cillosu a tare. Daga nan sai su canza wurin faɗawa. Wato wadda ta faɗa hannun dama da sai ta komo hannun hagu. Haka ma wadda ta faɗa hannun hagu za ta koma hannun dama. Za su riƙa yi suna waƙa kamar haka:

Kifi-kifi-kifi,

Kifin Malam Sale,

Ga daɗi ga kwaɗayi.

 

Shi ma Malam Sale,

Ga daɗi ga kwaɗayi.

Da zarar an kamala wannan waƙa, masu direwa za su koma cikin sauran ‘yanwasa. Wasu daban kuma za su fito tsakiya. 

6.90.2 Tsokaci

Wannan wasa yana sanya nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments