6.88 Goyon Kura
Wannan wasa yana da zubi da tsari irin na wasan goye-goye. Abin da ya bambanta su kawai shi ne yanayin goyon da ake yi. A goyon kura dai akan yi goyon ne a ranga-ranga. Wadda aka goya za ta kasance a kanta da ƙafafunta na gefe da gefe. Wadda ta yi goyon za ta riƙe ƙafafun da hannu ɗaya, sannan ta riƙe wuyanta da hannu guda.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.