Ticker

6/recent/ticker-posts

Goye-Goye

6.87 Goye-Goye 

Wannan ma wasan yara mata ne da suka fi gudanarwa a dandali. Yara biyu ne suke wasan goye-goye a tsakaninsu. Yayin da aka samu taron yara da yawa, kowacce za ta kama abokiyar goye-goyenta. Akan yi wannan zaɓi ne ta la’akari da girman jiki da kuma ƙarfi. Wato dai kowa takan kama daidai da ita, ƙwarya ta bi ƙwarya. Wannan wasa ne na dandali, saboda haka an fi gudanar da shi da dare, lokacin farin wata.

6.87.1 Yadda Ake Wasa

Yara sukan ƙiyasce wani wuri mai ɗan tazara a filin wasa. Wannan wuri shi ne za a riƙa zuwa. Daga nan ɗaya za ta goyi ɗaya ta nufi wurin da ita. Wasan na kasancewa idan yarinya ta goyi abokiyar wasanta zuwa can, to abokiyar ce za ta goyo ta ta dawo da ita. Wani lokaci kuma ana ‘yar zuwa da dawowa. Wato za a goyi yarinya a kai ta a dawo da ita. Daga nan ita ma sai ta rama wa abokiyarta.

6.87.2 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana samar da nishaɗi gare su.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments