Ticker

6/recent/ticker-posts

Shanyar Kuluri

6.86 Shanyar Kuluri

Wannan ma wasa ne na yara mata wadda ke tafiya da waƙa. Yana da ɗa daga cikin wasannin mata masu kasada da ƙiriniya. Yara uku ne suke gudanar da wannan wasa. Yana ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali. Kasancewar wasan na dandali ne, an fi gudanar da shi da dare, lokacin farin wata.

6.86.1 Yadda Ake Wasa

Akan goyi yarinya guda ɗaya. Sannan wadda aka goyan za ta banƙaro ta baya tamkar za ta faɗo. Sai yarinya ta uke, wadda da ma za ta tsaya a bayan wadda aka goya, ta kama hannuwanta. Ke nan za ta kasance tana reto a tsakankanin yaran biyu. Ɗaya na riƙe da ƙafafunta, ɗayan kuwa na riƙe da hannuwa. Za su riƙa tafiya suna waƙa kamar haka:

Bayarwa: Shanyar kuliri,

Amshi: Daka kuke.

 

Bayarwa: Kuke-kuke,

Amshi: Daka kuke.

Da zarar an ƙare iya zagayen da aka ƙiyasce za a yi wa yarinya, sai ta sauƙa wata kuma daban ta hau.

6.86.2 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su. Sai dai yana tattare da kasada, musamman yadda wani lokaci yarinyar da aka yi wa shanyar kuliri ke zamewa ta faɗo. Wani lokacin kuma yaran da ke riƙe da ita ne za su mata mugunta. Wato su sake ta da gangan ta faɗi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments