Ticker

6/recent/ticker-posts

Tambo

6.85 Tambo

Wannan ma wasa ne wadda take da zubi da tsari irin na babunna. Abu guda ne ya bambanta tsakaninsu. Wannan kuwa shi ne waƙar da ake gudanarwa cikin wasannin biyu. Wasan tambo dai ya fita daban da babunna da kuma sadam ta fuskar waƙa. Wannan kuwa ya faru ne kasancewar a wasan tambo akwai waƙoƙin iri-iri da ake yi, waɗanda suka danganta da kaɗin da ake. Waƙoƙin sun haɗa da:

Tambo tambo,

Tambo.

 

Tu wan tu wan tu wan,

Tuwan.

 

Tati tati-tati,

Tati.

 

Na sha na sha,

Na sha dirama.

 

O ba,

O bambalasta.

 

Ja ni ja ni,

Ja ni ga aikin ɗaya,

 

Ga aikin biyu,

Ga aikin uku.

 

Sakko sakko,

Sakko,

Sakkwato Illori,

Kaduna Maiduguri Legos,

Abuja, ya ci garin Legas,

Kaɗin ma had da iyawarsa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments