Ticker

6/recent/ticker-posts

Sadam

6.84 Sadam

Wannan wasa yana da zubi da tsari irin na babunna. Abubuwa biyu ne suka bambanta su. Na farko shi ne waƙar da ake yi yayin wasannin. Na biyu kuwa a wasan sadam ana harba ƙafa ne gaba a maimakon buɗewa ko tsukewa. A maimakon a buɗe ko a tsuke, a wasansa dama kan harba ƙafar dama ne ko ƙafar hagu. Waƙar da ake yi a cikin wannan wasa ita ce:

Sadam,

Sadam ya ce mu ware mu ware,

Maryam ta ce mu tsuke mu tsuke,

Ni kuma na ce mu harba a tare.

Duk sauran bayanan wasan sadam daidai suke da na tambo.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments