Ticker

6/recent/ticker-posts

Gariye

6.83 Gariye

Wannan ma wasan yara mata ne. Yana cikin rukunin wasannin gaɗa na dandali. Kimanin yara ashirin zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa. Wani lokaci yawan na gaza haka. Sai dai wasan ba ta daɗi idan masu gudanarwa ba su da yawa. Kasancewar wasan na dandali ne, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata.

6.83.1 Yadda Ake Wasa

Masu wasa za su yi da’ira mai faɗi ta hanayar barin‘yar tazara a tsakanin juna. Daga nan ɗaya za ta shigo tsakiya. Za ta riƙa bayar da waƙa saura kuwa suna amshi tare da tafi. Waƙar ita ce kamar haka:

Bayarwa: Duk garin nan,

Amshi: Gariye.

 

Bayarwa: Ba ni yaya,

Amshi: Gariye.

 

Bayarwa: Ba ni ƙanwa,

Amshi: Gariye.

Bayarwa: Sai ƙawata wadda muke mutunci,

Mutuncin ma mutunci.

Amshi: Gariye.

 

Bayarwa: Sai ƙawata Fati fito mu cashe,

Amshi: Gariye.

Bayarwa: Sai ƙawata Fati ki zo mu diske,

Amshi: Gariye.

 

Bayarwa/Amshi: Gariye na malilisi,

Gariye,

Girgiza wando,

Fatari siket,

Addinin‘yanmata.

Ke kika yarda?

Aka sa miki,

Girgiza wando?

Fatari, siket,

Addinin‘yanmata.

A wannan gaba, yara za su taka rawa su cashe. Daga nan kuma wadda ta ba da waƙa za ta kuma cikin sauran yara. Wata daban kuma za ta fito domin ba da waƙa.

6.83.2 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jini a gare su. A waƙar wasan na ƙara danƙon zumunci tsakanin ƙawaye. Duk wadda ƙawarta ta ambaci sunanta, za ta yi murna da farin ciki.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments