Ticker

6/recent/ticker-posts

Ruwaye

6.73 Ruwaye 

Wannan ma wasan dandali ne na gaɗa da aka fi gudanarwa da dare. Adadin masu gudanar da wannan wasa na kaiwa goma ko ma sama da haka. Yana tafiya da waƙa. Amma ba a buƙatar wani kayan aiki yayin gudanar da shi.

6.73.1 Yadda Ake Wasa

Yara sukan tsaya a tsarin da’ira. Sai su riƙa fitowa tsakiyar da’ira ɗaya bayan ɗaya suna ba da waƙa. Za su yi waƙar tare da sauran yara. Akan yi tafi da rangwaɗa yayin wannan waƙa. Ga yadda waƙar take:

Da ruwan sama za a yi soyayya,

In babu ruwa abu bai kyawo,

In sun yi yawa abu ya ɓaci,

Da masoyina nika soyayya,

Wanda bai ra’ayina ban nasa,

Da ruwa aka wanka in kanka,

Da ruwa ake wanke amarenmu,

In babu ruwa abu bai kyawo,

In sun yi yawa abu ya ɓaci,

Ke ku kira min Zainaba, Sadiya,

Ku kira min Ummi ga Ramatu,

In sun so za mu yi soyayya,

Babu tsince babu munafurci,

Ba ni jin maganar wasu sai tasu.

6.73.2 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sannan yana nuni zuwa ga muhimmanci da amfanin ruwa ga rayuwar al’umma. Baya ga wannan, waƙar wasan na ɗauke da saƙon sosayya ga masoya. Sannan masu wasan na ambaton sunayen makusantan abokansu, tare da nuna muhimmancinsu a rayuwa wurin shawara da yanke hukunci.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments