Ticker

6/recent/ticker-posts

Gyara Zamanki Kamar Ba Ke Ba

6.74 Gyara Zamanki Kamar Ba Ke Ba

Wannan ma wasan yara mata ne da ke buƙatar jama’a da yawa. Yawanci kimanin yara ashirin ne zuwa sama da haka suke gudanar da wannan wasa. Shi ma wasa ne da ke buƙatar garuruwa biyu. Wannan wasan dandali ne, saboda haka an fi gudanar da shi da dare, lokacin farin wata.

6.74.1 Yadda Ake Wasa

Yara sukan rabu zuwa gida biyu. Ko wane gari za su naɗa shugaba. Shugaban kowane gida za ta raɗa wa ‘yan gidanta sunaye. Akan yi amfani da sunayen kayan masarufi yayin wannan wasa. Sunayen sun haɗa da albasa da timatir da yakuwa da barkwano da tattasai da makamantansu. Da zarar an gama raɗa suna, sai shugabannin su yi canjin gida. Wato kowace za ta koma gidan abokan wasansu.

Daga nan shugabar gidan da za su fara yi za ta rufe wa ɗaya daga cikin‘yan gidan da ta koma idanu. Sai kuma ta kira ɗaya daga cikin‘yan gidanta, misali: “zogale.” Wadda aka naɗa wa suna zogale za ta taho ta doki kan wadda aka rufe wa idanu. Sai kuma ta koma da gudu ta zauna tamkar ba ita ta zo ta yi dukan ba. Dukkanin ‘yan gidan wadda ta yi dukan za su fara waƙa da tafi (har da wadda ta yi dukan) suna cewa:

Gyara zamanki kamar ba ke ba,

Gyara zamanki kamar ba ke ba.

Yayin da aka buɗe mata ido, za a ce ta je ta nuna wadda ta doke ta. Idan ta nuna daidai to wadda ta nuna ɗin za ta biyo ta zuwa gidansu. A irin wannan yanayi, akan ce ta jawo ta. Idan kuwa ba ta nuna daidai ba, ita ce za ta zauna a wancan gida. Ke nan ita an janye ta. Daga nan sai wancan gida su ma su yi haka nan. Haka dai za a yi ta yi har sai an janye wani gida ya zama na saura mutane ƙalilan. Daga nan ‘yan gidan da aka janye za su sha zolaya, har da zungura.

6.74.2 Sakamakon Wasa

Sakamakon wannan wasa shi ne tsokala da zungura. Waɗanda aka janye za su sha zolaya matuƙa. Waƙar da ake yi musu kuwa ita ce:

Mun ja su,

Mun ci su,

Mun sha su,

Mun nuna musu bambanci,

Ba da magani ba iyawa ne.

6.74.3 Tsokaci

Wannan wasa yana buƙatar nutsuwa da kuma amfani da tunani. Wadda aka doka sai ta yi nazari matuƙa kafin ta iya tantance wadda ta doke ta. Sannan wasan hanya ce ta samar da nishaɗi da annashuwa ga yara.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments