Ticker

6/recent/ticker-posts

Iye Nanaye

6.72 Iye Nanaye

Wannan wasa ne na yara mata. Yara biyu ma na iya gudanar da wannan wasa. Sai dai yawansu na iya wuce haka, zuwa huɗu ko shida ko takwas ko ma fin haka. Abin lura a nan shi ne, ‘yan wasan sukan kasance ne ta bibbiyu.

6.72.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko wurin biki ko wani wurin taron yaran mata.

ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma ko da dare, lokacin farin wata. Lokacin ya danganta da wurin da ake gudanar da wasan.

6.72.2 Yadda Ake Wasa

Yara biyu za su fuskanci juna. Sannan za su fara waƙa tare da tafi da kuma tsalle. A duk lokacin da suka yi tsalle a tare, ɗaya za ta mai da ƙafafunta zuwa ɓarin dama ɗaya kuma ta mayar da nata zuwa hagu. Ga yadda waƙar take:

Iye nanaye,

Ayyaraye iye,

Ayyaraye iye nanaye,

Mu je ke Fati,

Ai Fati na gida,

Ai Fati na gida,

Ba ta zo ba.

Ƙwaleru zai biya,

Ƙwaleru zai biya,

A ranar gobe,

Ƙwaleru zai biya,

Ƙwaleru zai biya wasanmu ragas.

6.72.3 Tsokaci

Wannan wasan hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan waƙar wasan na ɗauke da wani saƙo da ke nuni da al’adar Bahaushe inda samari ke biya wa ‘yan matansu kuɗi irin na kwalliya da ashobe da makamantansu.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments