Ticker

6/recent/ticker-posts

Son Makaru

6.71 Son  Makaru

Wannan ma wasa ne na dandali. Yawanci mutane goma zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa.

6.71.1 Wuri Da Lokacin Wasa

An fi gudanar da wannan wasa a dandali, musamman da dare lokacin farin wata.

6.71.2 Yadda Ake Wasa

Masu wasa za su yi da’ira amma kusa da juna. Daga nan kowace za ta buɗa hannuwanta zuwa gefe da gefe. Kowacce za ta ɗora hannunta na dama a kan tafin hannun wadda ke gefenta. Ita ma za a ɗora hannu bisa hannunta na hagu. Daga nan za a fara waƙa kamar haka:

Son makaru,

Son file mi lo,

Maliyo-maliyo alewa-alewa,

Cus-cus-cus,

Alewar baba akwai daɗi.

Ɗaya,

Biyu,

Uku.

Yayin da ake wannan ƙirge, kowace za ta riƙa kawo tafi da hannunta na dama. Ma’ana za ta tafa da hannunta na dama da hannun hagu da wadda ke gefenta. Idan ta tafa sau uku a daidai, to ta fita. Daga nan sai ta koma gefe ta sa wa saura ido. Wannan wasa ba shi da sakamako.

6.71.3 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi da annashuwa ga masu gudanarwa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments