Ticker

6/recent/ticker-posts

Maimuna Ta Yi Ciki Ga Goyo

6.7 Maimuna Ta Yi Ciki Ga Goyo

Wannan wasan ma na tashe ne. ‘Yanmata na gudanar da shi cikin watan azumi.

6.7.1 Lokaci Da Wurin Wasa

1. An fi gudanar da shi da dare. Wasu ɗaiɗaikun lokuta akan gudanar da shi da hantsi ko yamma.

2. Masu wasa sukan shiga gida-gida domin gabatarwa.

6.7.2 Kayan Aiki

1. Tsummokara

2. ‘Yartsana ko wani abu a matsayin jinjiri/jinjira

3. Ganye (kamar ganyen maina/darbejiya, irin wanda ake wankan jego da shi)

6.7.3 Yadda Ake Gudanar Da Wasa

Ɗaya daga cikin yara (Maimuna), na sanya tsummokara cikin riga, daidai cikinta. Cikin zai yi girma tamkar dai mai ciki. Sannan za ta goyi ‘yartsana, ko dai wani abu da zai kasance a matsayin ɗa. Sauran yaran kuwa za su riƙe ganyen bishiya a hannunsu (mafiyawanci na maina/darbejiya). Daga nan za su riƙa bi gida-gida, wasu daga cikin ‘yan matan suna ba da waƙa saura na amsawa, sannan suna yarfa mata ganyayyakin da ke hannunsu. Ita kuwa za ta ci gaba da tafiya irin ta masu ciki tare da jijjiga goyon da ke bayanta.

6.7.4 Waƙar Wasa

Bayarwa: Maimuna ta yi ciki.

Amshi: Maimuna ba ta tsoron wanka. 

6.7.5 Tsokaci

Wannan wasa yana nuna al’adar Bahaushe ta haihuwa da goyo da kuma wankan jego. Sannan za a iya kallon ɓirɓishin rashin gamsuwar Bahaushe ga Haihuwa marar tsari.

WASANNI A ƘASAR HAUSA 

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments