Ticker

6/recent/ticker-posts

Matar Nakarofi

6.6 Matar Nakarofi

Wannan ma wasan tashe ne da ‘yan mata ke gudanarwa a watan azumi. Masu gudanarwar sukan kai biyar zuwa sama.

6.6.1 Lokaci Da WurinWasa

i. Da shike wasan tashe ne da ake gudanarwa cikin watan azumi, an fi yin sa da dare. Amma wasu lokuta akan gudanar da shi da hantsi ko kuma da yamma.

ii. ‘Yan mata sukan bi gida-gida domin gudanar da wannan wasan tashe.

6.6.2 Kayan Aiki

i. Tabarma da buta da kwanoni da kayan ɗaki da kuma makamantansu

ii. Kayan maza, kamar malum-malum da wando da hula

iii. Kayan shafe-shafe na kwalliyar mata

6.6.3 Yadda Ake Gudanar Da Wasa

Ɗaya daga cikin‘yanmatan (Matar Nakarofi) na shiga irin ta amare. Wato takan caɓa ado sannan ta yi lulluɓin kai. Akan samu wata kuma ta yi shigar maza. Wato ta sanya malum-malum da hula da wando. Sannan yaran kan tafi da tabarma da kwanuka da buta da makamantansu (kayan ɗakin amarya). Da zarar sun shiga gida, za su shimfiɗa tabarmar sannan su jera kwanukan tsaf, a matsayin ɗakin amarya. Daga nan Matar Karofi  za ta zauna bisa tabarmar, sannan wadda ta sanya kayan maza za ta zauna gefenta, a matsayin miji. Daga nan kuma mai kayan mazan (miji) za ta fara waƙa, yayin da sauran ‘yan matan za su riƙa amsawa. Misali:

Miji: Matar Nakarofi,

Matar Nakaro ba shawara.

‘Yan mata: Tashe!

 

Miji: Jiya na yi amarya ta kwana a shingen dankali.

‘Yan mata: Tashe!

 

Miji: Shashashar banza mai kwana a shingen dankali.

‘Yan mata: Tashe!

Miji: Ba ni aurenki tun da kin kwana a shingen dankali.

‘Yan mata: Tashe! 

Da zarar matar Nakarofi ta ji haka, sai ta yi fushi. Daga nan za ta tashi fuuu cikin fushi, ta yi yaji zuwa gidansu (wato wani gefe guda). Haka na faruwa mijin Nakarofi za ta sake ba da waƙa, saura kuma na amsawa:

Miji: Ku yo mini bikon matar Nakarofi,

Matar Nakarofi ba shawara.

‘Yan mata: Tashe! 

Daga nan wasu daga cikin ‘yan matan za su je gidansu matar Nakarofi domin biko. Amma za ta ƙi tahowa. Saboda haka dole mijin Nakarofi ta je da kanta. A can gidansu matar Nakarofi (wurin da take zaune), mijin matar Nakarofi za ta fara waƙa, sauran mata na amsawa. Misali:

Miji: Ga buhun kitso nan na tuba,

Ki gafarce ni.

‘Yan mata: Tashe!

 

Miji: Ga buhun fura nan na tuba,

Ki gafarce ni.

‘Yan mata: Tashe!

 

Miji: Ga buhun rama nan na tuba,

Ki gafarce ni.

‘Yan mata: Tashe!

 

Miji: Ga buhun daddawa nan na tuba,

Ki gafarce ni.

‘Yan mata: Tashe!

Haka wannan biko zai ci gba har sai an sallame su. 

6.6.5 Tsokaci

Wannan wasan na faɗakarwa zuwa ga tauna magana kafin furta ta, kamar yadda mijin matar Nakarofi ta ja wa kanta jangwangwan. Sannan wasan na fitar da al’adar Bahaushe ta yaji da biko a cikin aure. Bayan haka akwai nishaɗantarwa a cikin wasan. Ko ban da yadda ‘yan matan ke tsara ɗakin amaryar, waƙar bikon kanta abin dariya ce. Wane gwani ne yake iya ƙulla buhun kitso da kuma buhun fura?

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments