Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Da ‘Yata

6.8 Ina Da ‘Yata

Wannan wasa ne na dandali. Yara mata da kuma ‘yanmata duk sukan gudanar da wannan wasa.

6.8.1 Lokaci Da Wurin Wasa

i. Ana gudanar da wannan wasa ne da dare, musamman lokacin farin wata.

ii. Akan gudanar da wannan wasa a dandali, ko kuma filin gaban gida.

6.8.2 Yadda Ake Gudanar Da Wasa

Yayin da yara ko ‘yan mata suka taru, ɗaya daga cikinsu za ta riƙa ba da waƙa, saura kuma suna amsawa. Ga yadda abin yake:

Jagora: Ayyaranaye, ayyayare yarayenaye.

‘Y/Amshi: Iyaranaye ayyaraye yaraye nanaye.

 

Jagora: Ina da ‘yata da ba za ni ba mai farauta ba.

‘Y/Amshi: Me ye dalilin da ba za ki ba mai farauta ba?

 

Jagora: Wuni a daji kwana a daji kamar kura.

‘Y/Amshi: Iyaranaye ayyaraye yaraye nanaye.

 

Jagora: Ina da ‘yata da ba za ni ba malamin bana ba.

‘Y/Amshi: Mai dalilin da ba za ki ba malamin bana ba?

 

Jagora: Wuni karatu amma idon a kan mata.

‘Y/Amshi: Iyaranaye ayyaraye yaraye nanaye.

 

Jagora: Ina da ‘yata da ba za ni ba ɗan giya ba.

‘Y/Amshi: Mai dalilin da ba za ki ba ɗan giya ba?

 

Jagora: Wuni a maye, kwana a maye yana wari,

‘Y/Amshi: Iyaranaye ayyaraye yaraye nanaye.

 

Jagora: Ina da ‘yata, ba za ni ba wa wanzami ba.

‘Y/Amshi: Mai dalilin da ba za ki ba wa wanzami ba?

 

Jagora: Kwana da aska bai aske gashin baki ba,

‘Y/Amshi: Iyaranaye ayyaraye yaraye nanaye.

 

Jagora: Ina da ‘yata ba za ni ba wa maroƙi ba,

‘Y/Amshi: Mai dalilin da ba za ki ba wa maroƙi ba?

 

Jagora: Wuni da ganga, bai yi tsubin ƙima ba.

‘Y/Amshi: Iyaranaye ayyaraye yaraye nanaye.

6.8.3 Tsokaci

Wannan wasa na ɗauke da taƙaitaccen tsokaci game da wasu sana’o’in Hausawa, tare da hannunka-mai-sanda ga masu sana’ar. Sannan yana faɗakarwa game da wasu halayya waɗanda suka kasance ababan ƙi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments