Ticker

6/recent/ticker-posts

Afurka-Afurka

6.68 Afurka-Afurka

Wannan wasa ma na dandali ne. Kimanin yara mata goma ne zuwa sama da haka suke gudanar da shi. Sai dai wani lokaci akan samu ƙasa da wannan adadi.

6.68.1 Wuri Da Lokacin Wasa

Akan gudanar da wannan wasa ne a dandali, musamman da dare lokacin farin wata.

6.68.2 Yadda Ake Wasa

Masu wasa za su yi da’ira ba mai faɗi ba. Wato dai za su tsaya kusa da juna. Daga nan za a fara waƙa tare da tafi. Waƙar ita ce kamar haka:

Afurka-Afurka yoyoyo,

Afurkan benda-benda,

O benda.

O benda.

Da zarar an zo wannan gaɓa, wadda za ta fara wasa za ta ɗan duƙa. Ta gefen hagu da damanta za su tafa bisa kanta. Daga nan za ta tashi. Sai kuma ta gefenta ta duƙa. Ita ma za ta tafa bisa kanta. Haka za a yi ta zagayawa. Duk wadda ta ɓata, to za ta fita waje. Haka za a yi ta raguwa har sai an dawo mutane biyu. Su ma za su yi tsakaninsu, har sai ɗaya ta ɓata. Daga nan sai a dawo a sake wasa daga farko. Wasan ba shi da sakamako.

6.68.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan wasan na buƙatar nutsuwa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA 

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments