Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwalliyar La’asar

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

6.69 Kwalliyar La’asar

Wannan ma wasan gaɗa ne da ake gabatarwa a dandali. Yana tafiya da waƙa. Ba a buƙatar wani kayan aiki domin gudanar da shi. Yawanci akan samu adadin yara da yawa yayin gudanar da wasan. Yawansu na iya kaiwa goma sha biyar ko ashirin ko ma sama da haka. Kasancewarsa wasan gaɗa na dandali, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata.

6.69.1 Yadda Ake Wasa

Masu wasa za su yi da’ira. Daga nan sai su fara fitowa cikin da’ira ɗaya bayan ɗaya. Za su riƙa waƙa tare da tafi da kuma ‘yar rawa da rangwaɗa. Ga yadda waƙar take:

Kwalliyar la’asar yarinya kwalliyar la’asar,

Na biya hanya sai na ga farar ɗiya mai kyawun kallo,

Wannan yarinya ko Sakkwato ta ciyo lambar gayu,

Da ta shigo leshi wagambari ga abin ɗauri ta sha,

Da ta zagaye ta ce masa wawa jaki ba ni wuri,

Tun da jaki ne, ki aro mana shi mu kai taki gona!

Da gargada da kwana duk ɗai suke in ji mai tuƙin jirgi,

Wannan yarinya har Sakkwato ta ciyo lambar girma,

A zaɓi yarinyar kwalliyar la’asar ta fi.

Kwalliyar la’asar yarinya ta lashe,

Ta bar saura suna cizon hannu,

Kwalliyar la’asar yarinya kwalliyar la’asar.

6.69.2 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sannan yana isar da saƙo game da tsafta da ado. An kuma yi amfani da salo mai armashi ciki, ta hanyar sanyo zancen raha. A dai tausaya wa jakin kada a riƙa lafta masa kaya.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Post a Comment

0 Comments