Ticker

6/recent/ticker-posts

Jar Miya

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

6.67 Jar  Miya 

Wannan ma wasan gaɗa ne da ke buƙatar ‘yan wasa da dama. Misalin mutane ashirin ne zuwa sama da haka suke taruwa domin gudanar da shi.

6.67.1 Wuri Da Lokacin Wasa

Kasancewar wasan na gaɗa kuma na dandali, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata.

6.67.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan yi da’ira mai ɗan faɗi. Daga nan ɗaya za ta fito tsakiyar da’irar. Za ta riƙa ba da waƙa sauran kuma suna amsawa tare da tafi da rangwaɗa. Ga waƙar kamar haka:

Waƙa: Jar miya zan aura,

Amshi: In babu jar miya me zan yi da koriya?

Waƙa: Uwar miji ta zagen,

Amshi: Na durƙusa ina nema mata gafara. 

A wannan gaɓa dukkanin ‘yan wasa za su durƙusa ƙasa, tamkar dai suna nema mata gafarar da gaske. Waƙa kuma za ta ci gaba kamar haka:

Waƙa: Uban miji ya zagen,

Amshi: Na durƙusa ina nema masa gafara.

Waƙa: Kishiya ta zagen,

Amshi: Na lillisa ta na juya ta,

Na kai ta ofishin‘Yansanda,

Sun lillisa ta sun juya ta,

Shegiya‘yar banza,

Sun kai ta lahira sai ga ta a duniya,

Shegiya‘yar banza.

Da zarar an kawo wannan gaɓa, to wadda take tsakiya za ta koma cikin da’ira. Wata daban kuma za ta fito domin ci gaba da wasa.

6.67.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan waƙar wasan na ɗauke da wani saƙo da ya kasance tamkar madubin hasko al’adar Bahaushe na biyayya da ladabi ga na gaba da shi. A ɓangare ɗaya kuma, waƙar na nuna irin kishin da ke tsakanin kishiyoyi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Post a Comment

0 Comments