Ticker

6/recent/ticker-posts

Ke Kika Je Gidansu Direba

6.66 Ke Kika  Je Gidansu Direba

Wannan wasan mata ne da ke tafiya da waƙa. Yana ɗaya daga cikin wasannin tashe na yara mata. Sannan akan bukaci kayan aiki yayin gudanar da shi. Kimanin yara biyar zuwa sama ne suke gudanar da wasan.

6.66.1 Wuri Da LokacinWasa

i. Akan bi gida-gida ne domin gudanar da wannan wasa.

ii. Akan yi wannan wasa da hantsi ko da yamma. Wasu lokuta kuma akan yi shi da dare kamar sauran wasannin tashe.

6.66.2 Kayan Aiki

i. Tsummokara

ii. Foda ko wani abin shafawa a fuska

iii. Zane (domin ɗaure tsummokara a ciki)

6.66.3 Yadda Ake Wasa

Yara za su yi wa ɗayarsu cikin tsummokara. Za su ɗaure tamau da wani zane, yadda ba zai ware ba. Shigar za ta yi tamkar dai mai cikin gaske. Sannan za a shafa mata foda ko wani abu da zai kalance mata fuska. Daga nan za su ɗunguma zuwa gidan tashe.

Yayin da suke gidan domin tashe, za su fara waƙa da ke nuna wannan yarinya ta yi cikin shege ne. Ita kuwa za ta riƙa bayyana da-na-sani game da cikin da ta yi da kuma dalilin da ya ja ta zuwa wannan yanayi, duk dai cikin waƙa. Ga yadda waƙar take:

Yara: Ke kika je ki gidansu direba,

Mai Ciki: Da ban je ba ina zan samu?

Kullum biredi kullum shayi,

Kullum tsire yanka goma,

Na je likita ya auna ni,

Ya ce cikin direbobi ne,

Wayyo direba ka cuce ni,

Wayyo direba ka ci amana.

Haka za su ci gaba da wannan waƙa. Har sai an ba su abin sadaka, ko kuma an sallame su ta hanyar ba su haƙuri. Wani lokaci yaran har zungurar wannan yarinya da ta yi ciki suke yi.

6.66.4 Tsokaci

Wannan wasa na samar da annashuwa musamman ga masu kallo. Sannan wasan na faɗakarwa ne game da wani hali da ya ci karo da al’ada da Addinin Bahaushe. Ana nuna cewa, kwaɗayi na kai mutane ga halaka.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments