Ticker

6/recent/ticker-posts

Yaraye Dije

6.65 Yaraye Dije 

Wannan ma wasan gaɗa ne na dandali da ke buƙatar mutane da yawa domin gudanar da shi. Yawansu na iya kaiwa ashirin ko ma sama da haka. Kasancewar wasan na gaɗa kuma na dandali, an fi gudanar da shi da dare, lokacin farin wata.

6.65.1 Yadda Ake Wasa

Yara za su yi da’ira mai ɗan faɗi ta hanyar barin tazara tsakanin junansu. Daga nan ɗaya za ta fito tsakiyar da’ira, sannan ta riƙa ba da waƙa. Sauran za su riƙa amsawa tare da tafi da rangwaɗa. Waƙar ita ce kamar haka:

Waƙa: Ayye yaraye iye Dije.

Amshi: Ayye yaraye iye Dije.

 

Waƙa: Wai ta ce gidansu ba yunwa,

Amshi: Wai ta ce gidansu ba yunwa.

Waƙa: Sai na ga yakuwa tana dakon ƙanzo,

Amshi: Tubalin gaye.

6.65.2 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana samar da nishaɗi da annashuwa gare su. Waƙar wannan wasa na ɗauke da habaici, kamar yadda wata ta nuna babu yunwa a gidansu. Sai kuma ga shi an tarar da za a yi gwaten/faten ƙanzo da yakuwa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments