Ticker

6/recent/ticker-posts

Tattaba-Tattaba

6.64 Tattaba-Tattaba 

Wannan wasan yara mata ne da ke tafiya da waƙa. Ba a buƙatar kayan aiki yayin da ake gudanar da shi. Kimanin mutane goma zuwa sama da haka ne ke gudanar da wannan wasa. Da yake wasan gaɗa ne na dandali, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata.

6.64.1 Yadda Ake Wasa

Yara za su jeru a tsaye cikin tsarin da’ira. Sai kuma su riƙa fitowa ɗaya bayan ɗaya suna waƙa. A cikin waƙar sukan ambaci sunayen ƙawaye da masoya da kuma wasu ‘yanuwa kamar ƙanne da yayu. Sauran yara kuwa za su riƙa amsawa tare da tafi da bugun cinya. Ga waƙar kamar haka:

Bayarwa: Tattaba-tattaba,

Amshi: Ayye tattaba-tattaba ye.

 

Bayarwa: Ni ƙanuwar Khalid,

Amshi: Kin ci fure kin goge haƙora fes.

Bayarwa: Ƙanuwar Khalid fara mai kyawo,

Amshi: Kin ci fure kin goge haƙora fes.

 

Bayarwa: Ayye ni yayar Zainab,

Amshi: Kin ci fure kin goge haƙora fes.

 

Bayarwa: Ayye ni ƙawa ga Hadiza,

Amshi: Kin ci fure kin goge haƙora fes.

 

Bayarwa: Ayye ni ƙawa ga Sakina,

Amshi: Kin ci fure kin goge haƙora fes.

 

Bayarwa: Ayye na ci fure na goge haƙora fes,

Amshi: Kin ci fure kin goge haƙora fes.

6.64.2 Tsokaci

Wannan wasa yana motsa jiki tare da samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta ƙara danƙon‘yanuwantaka da zumunci tsakanin‘yanuwa da kuma ƙawaye. Duk wadda wata ta ambaci sunanta, za ta ji daɗin kasancewar an riƙe ta a matsayin ƙawa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments