Ticker

6/recent/ticker-posts

Salo-Salo

6.62 Salo-Salo

Wannan ma wasa ne na mata da ke tafiya da waƙa. Ba a buƙatar wani kayan aiki yayin gudanar da shi. Yawanci akan samu adadin yara da yawa yayin gudanar da wasan. Wani lokaci yawansu na kaiwa ashirin ko ma sama da haka.

6.62.1 Wuri Da LokacinWasa

i. An fi gudanar da wannan wasa a dandali, musamman lokacin farin wata.

ii. Akan yi wannan wasa ne da dare. Sai kuma a ɗaiɗaikun lokuta akan yi shi da yamma musamman a gidajen biki, yayin da aka samu taron yara mata.

6.62.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan tsaya bisa tsarin da’ira. Ɗaya daga cikinsu za ta fito ta riƙa nuna su ɗaya bayan ɗaya cikin rangwaɗa. Za ta riƙa zagaya cikin da’irar yayin da take nuna su. Sanan za ta riƙa ba da waƙa. Sauran ‘yan wasa kuma za su riƙa amsawa tare da tafi. Waƙar kuwa tana da tsari kamar haka:

Waƙa: Salo-salo,

Amshi: Salo.

 

Waƙa: Wannan tawa ce,

Amshi: Salo.

 

Waƙa: Ke ma tawa ce,

Amshi: Salo.

 

Waƙa: Ke ma tawa ce,

Amshi: Salo.

 

Waƙa: Ke da na rena ba ni ce miki tawa ce,

Amshi: Salo.

 

Waƙa: Mai satar wuri,

Amshi: Salo.

 

Waƙa: To mene ne wuri,

Amshi: Salo.

 

Waƙa: Ke kika san wuri har kina sata tasa,

Amshi: Salo.

 

Waƙa: Karya ƙashin wuya,

Amshi: Salo.

 

Waƙa: Har da na kafaɗa,

Amshi: Salo.

 

Waƙa: Har da na kwankwaso,

Amshi: Salo. 

Yayin da aka iso wannan gaɓa, yara za su taka rawa sosai su cashe. Idan aka ambaci: “Karya ƙashin wuya,” za su riƙa jijjiga kai tamkar ka ce su tsinke shi. Haka ma yayin da aka ce: “Har da na kafaɗa,” za su yi rawa da kafaɗa. Haka ma yayin da aka ambaci; “Har da na kwankwaso.”

6.62.3 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki ga yara. A cikin waƙar wasan, yara suna nuna danƙon abota da ke tsakanin junansu.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments