Ticker

6/recent/ticker-posts

Alo NaTaro Na Tattaro

6.63 Alo NaTaro Na Tattaro

Wannan ma wasan gaɗa ne da ke buƙatar ‘yan wasa da yawa. Yawanci masu wasa sukan kai ashirin zuwa sama da haka. Yana cikin jerin wasannin yara mata da ke tafiya da waƙa. Sai dai ba ya buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi.

6.63.1 Wuri Da Lokacin Wasa

Alo nataro na tattaro wasan gaɗa ne na dandali. An fi gudanar da shi da dare lokacin farin wata.

6.63.2 Yadda Ake Wasa

Masu wasa sukan yi da’ira mai ɗan faɗi. Daga nan yarinya ɗaya za ta fito tsakiya. Za ta riƙa ba da waƙa yayin da saura ke amsawa tare da tafi da rangwaɗa. Waƙar ita ce kamar haka:

Waƙa: Alo nataro na tattaro,

Amshi: Wa kika tattaro ne?

 

Waƙa: Alo nadaka na tankaɗe,

Amshi: Wa kika bai tsaki ne?

 

Waƙa: Iye na bai wa A’i,

Amshi: Kuma du,

 

Waƙa: Na bai wa Khalid,

Amshi: Kuma du,

 

Waƙa: Na bai wa Sadi,

Amshi: Kuma du,

 

Waƙa: Na bai wa Nana.

Wayyo ni Nana,

Hasken rayuwata,

Din na ga babu Nana,

Sai na rabsa kuka,

Dis nagidan fulawa,

Sai babanWasila,

Kadi namari kamar mari,

Komai ya yi daidai.

Da an kawo wannan gaɓa mai yi ta ƙare yin ta. Daga nan wata daban za ta shigo domin a ci gaba da wasa.

6.63.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana samar da nishaɗi gare su. Waƙar wannan wasa na ɗauke da sunayen ‘yanuwa (ƙanne da yayu) na mai waƙar. Sannan tana nuna yadda mai waƙar ta ɗauki ‘yanuwantaka da muhimmanci.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments