Ticker

6/recent/ticker-posts

Karya Gadidi

6.61 Karya Gaɗiɗi

Wannan wasan gaɗa ne mai zubi da tsari irin na rowan ƙauye. Mutane biyar zuwa sama da haka ke gudanar da shi.

6.61.1 Wuri Da Lokacin Wasa

Wannan wasa ne na dandali. Saboda haka an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata.

6.61.2 Yadda Ake Wasa

Yara na tsayawa manne da juna a layi ɗaya. Daga nan sai guda ɗaya ta kasance a gabansu. Za su riƙa waƙa da tafi yayin da wannan yarinya da ke gaba za ta riƙa faɗowa jikinsu. Su kuwa za su riƙa tallabarta suna cillo ta gaba. Haka za a ci gaba da yi har sai an kai ƙarshen waƙa.

Wasan bai tanadi suna na musamman ba ga ɓangarorin masu wasa. Amma wannan Littafi ya ba wa wadda ke gaba suna mai direwa. Waɗanda ke layi guda kuma ya kira su da masu cilli. Ga yadda waƙar take:

Mai Direwa: Karya gaɗiɗi,

Karya gaɗiɗi.

Masu Cilli: Garya gaɗis!

Kainuwa.

 

Mai Direwa: Kainuwa dashen Allah,

Masu Cilli: Kainuwa.

 

Mai Direwa: Ba dashen mutane ba,

Masu Cilli: In dashen mutane na.

Mai Direwa: Ko ruwa ba na sha ba.

Masu Cilli: Kainuwa.

 

Mai Direwa: Ko kunu ba na sha ba.

Masu Cilli: Ya ishe ki yar Malam Adamu,

Ya ishe ki ‘yar MalamAdamu.

Da zarar an kawo wannan gaɓa, to yin mai direwa ya ƙare. Sai ta fita, wata kuma ta shigo.

6.61.3 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi da motsa jiki ga yara. Sannan waƙar wasan na ɗauke da hannuka-mai-sanda kan cewa duk Ubangiji ne kaɗai ke da ikon yin yadda Ya ga dama ga rayuwar mutum. Sannan Shi ke bayarwa kuma Shi ke hanawa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments