Ticker

6/recent/ticker-posts

Bakutu Mai Babban Duwawu

6.5 Ɓakutu Mai Babban Ɗuwawu

Ɓakutu dai laƙabi ne da ake yi wa yarinya mai ƙiba da kuma gajeren wuya. Wannan ma wasan tashe ne da yara mata ke gudanarwa a cikin watan azumi. Yawan masu gudanar da wannan wasa na iya kai biyar ko sama da haka.

6.5.1 Lokaci Da Wurin Wasa

i. An fi gudanar da wannan wasa da dare bayan an sha ruwa, cikin watan azumi. Amma wasu lokuta akan yi tashen Ɓakutu da hantsi ko da yamma.

ii. Wasan Ɓakutu ba shi da wuri taƙamaimai. Yara na bin gida-gida ne domin aiwatarwa.

6.5.2 Kayan Aiki

i. Tsummokara ko filo/matashin kai

6.5.3 Yadda Ake Gudanar Da Wasa

Yarinya ɗaya (Ɓakutu) takan yi duwawun tsummokara. Ma’ana ta sanya tsummokara yadda duwawunta zai yi tudu sosai. Daga nan za ta wuce gaba sauran ‘yan mata kuma su bi ta a baya. Za ta riƙa ‘yar rawa tana juyi da ƙyar, sannan tana taku ɗaiɗai, tamkar dai yadda mai ƙiba ta haƙiƙa ke yi. Yaran za su riƙa ba da waƙa suna amsawa, yayin da Ɓakutu kuwa take ta fama da tafiya da ƙyar saboda ƙiba. Haka za su riƙa yi har sai an sallame su.

6.5.4 Waƙar Wasa

Masu Bayarwa: Ɓakutu mai babban ɗuwawu.

Y/Amsohi: An huta da sayen kujera!

Masu Bayarwa: Ɓakutu mai babban ɗuwawu.

‘Y/Amshi: Bana mun huta da siyen kujera

6.5.5 Tsokaci

Wannan wasa yana ɗauke da raha da ban dariya, musamman idan masu kallo suka ga yadda Ɓakutu take ta faman rawa da manyan ɗuwawunta da take juya su da kyar.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments