Ticker

6/recent/ticker-posts

A Cikin Wannan Rana

6.58 A CikinWannan Rana

Wannan wasa ne da ke da zubi da tsari iri guda da wasan Gamuna da aka tattauna ƙarƙashin 6.40. Sai dai waƙar da ake yi ciki ta bambanta kwata-kwata da waƙar wasan Gamuna.Waƙar da yara ke yi a wasan a cikin wannan rana ita ce:

Masu Ɗauka: Assalamu alaikum a cikin wannan rana,

Masu Bayarwa: Wa alaikumussalam a cikin wannan rana.

 

Masu Ɗauka: Ga mu mun zo gare ku a cikin wannan rana,

Masu Bayarwa: Meye dalilin zuwanku a cikin wannan rana?

 

Masu Ɗauka:  Akwai dalilin zuwanmu a cikin wannan rana,

Masu Bayarwa: Sai ku faɗa mana dalili.

 

Masu Ɗauka: Ɗiyarku ce muke so a cikin wannan rana,

Masu Bayarwa: Sai ku faɗa mana sunanta a cikin wannan rana.

 

Masu Ɗauka: Sunanta Khadija,

Masu Bayarwa: Sai ku ɗauko mun ba ku,

Kar ku bar ta da yunwa,

Mu gidanmu ba yunwa,

Mu gidanmu ba dauɗa,

A cikin wannan rana.

 

Masu Ɗauka: Mun gode mun gode,

A cikin wannan rana.

Kamar yadda aka ambata a sama, wasan yana da zubi da tsari irin na wasan Gamuna. Saboda haka, ba ya buƙatar wani dogon bayani.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments